Jaririyar da aka tsinta a Kaduna ta samu iyayen riƙo a Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Wasu ma'aurata ƴan Najeriya mazauna Amurka sun karɓi riƙon wata jaririya da aka tsinta a unguwar Rigasa da ke Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya.
A ranar Asabar ne mai shafin Northern Hibiscuss a Instagram Aisha Falke ta wallafa labarin cewa wata mata mai bin shafin ta tuntuɓe ta cewa an tsinci jaririya a kusa da gidanta.
A hirar da BBC ta yi da Aisha Falke ta ce matar ta kira ta ne, "sai ta ce min 'Malama yarana suna ƙwallo sai suka ji kukan jaririya sai muka je muka ga jaririya ce sabuwar haihuwa aka ajiye a can wani gefe na filin ƙwallon', a cewarta.
Daga nan ne suka tafi ofishin ƴan sanda inda su kuma suka ce wa matar ta je Allah ne Ya ba ta, ita kuma ganin a yanzu haka tana jegon ƴan biyu ta ce gaskiya ba za ta iya ba.
Sai ta kira Aisha Falke ganin cewa ita ɗin tana yawan yin magana kan karɓar riƙon ƴaƴa. Ita kuma sai ta wallafa a shafinta da zummar yin cigiya ko za a samu masu karɓar riƙonta.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram
Sai dai babu wani ƙoƙari da hukumomin suka yi don bin sawu ko diddigi kan ko za a dace a gano wanda ya jefar da jaririyar.
Aisha Falke ta ce matar ta shaida mata cewa an kira ƙwararru kan harkar lafiya waɗanda suka tabbatar da cewa jaririyar sabuwar haihuwa ce don ba ta wuce awa uku ba a lokacin da aka tsince ta.
"Cibiyarta ma na ta ɗigar jini a lokacin kuma bakwaini ce. Sai muka yi mata wanka muka sanya mata kaya don ta ji ɗumi, muka kuma ba ta madara ta sha," kamar yadda matar ta shaida.
Kwana guda bayan wallafa cigiyar neman iyayen riƙon ne sai aka samu iyalai fiye da 100 da suka nemi Aisha Falke kan son karɓar jaririyar a cewar mai shafin na Northern Hibiscuss.
A ƙarshe dai a ranar Lahadi aka samu aka daidaita da wasu ma'aurata ƴan Najeriya mazauna Amurka da suka nuna sha'awar karɓar ƴar.
"Sun wakilta danginsu da ke Kaduna aka je wajen ƴan sanda aka kammala dukkan wasu yarjejeniya aka damƙa musu ita.
"A yanzu haka har sun yi mata huɗuba da suna Amina Jamilah, kuma sabbin iyayen nata za su taho Najeriya a cikin makon nan don su zo su tafi da ita," in ji Aisha.

Ta ƙara da cewa dama su ma'auratan kwanan nan suka haifi yarinya kuma ta rasu, "wallahi ba ki ga zumuɗin da suke yi ba tun da muka yi waya aka fara maganar sun shiga cikin farin ciki da walwala.
"Na dade ban ga murnar dan Adam ba kamar yanda adoptive mother (yar aji) din ta nuna ba jiya da daddare. Habawa!!!! Na ringa ce mata calm down calm down," kamar yadda Falke ta rubuta a shafinta.
Falke ta ce wannan lamari ya matuƙar faranta mata rai da kuma godiya ga ƴar ajinta da ta tsinci jaririyar.
Dama an ce komai da sila. Wannan abu ya faranta min rai. ALLAH ya yi baby din tasu ce shi ya sa a ka ajiye ta din. Da rabon su za ta rayu.
"Ba abin da yake faruwa ba tare da Allah Ya tsara shi ba. Allah Shi ne mafi sani.
Ta ƙara da cewa ba ta taɓa sanin cewa mutane sun damu sosai da son ɗaukar riƙon ƴaƴa ba musamman waɗanda ba su haɗa komai da su ba sai da wannan lmari ya faru.
Falke ta kuma sha alwashin cewa tun da akwai irin wadannan yara da yawa musamman a gidajen marayu, to za ta yi iya ƙoƙrinta don ganin ta yi wa masu neman riƙon ƴaƴa hanya sun samu waɗanda za su riƙe idan Allah ya so.

Me ya sa ake jefar da ƴaƴa a arewa
Al'adar jefar da jarirai lamari ne da ya zama ruwan dare a arewacin Najeriya, inda a baya aka sha tsintar su ko dai bola ko a kwangaye, wasu lokutan kuma a kan tsinci gawarsu ne a masai ko kwata ko kududdufi.
A tsarin rayuwar Bahaushe, babu wani abu da ya fi takaici da kunya irin a ce mace ta yi ciki ba tare da aure ba.
Hakan ce ta sa idan har irin wannan kaddara ta fada wa wasu, sai su yi duk kokarin da za su yi don gujewa haifar cikin.
Gudun tsangwama da kyara ne yake sa a lokuta da dama mata ke irin hakan. Sau tari kuma ma ba macen ce da kanta take jefar da yaron ba, iyayenta ne suke ƙwacewa su jefar don gudun ɓata sunan zuri'arsu.












