Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda mata ke iya adana ƙwayayen haihuwarsu saboda gudun lokaci ya wuce
A faɗin duniya, mata da dama sun fara ɗaukar matakin adana ƙwayayensu na haihuwa don gudun wucewar lokacin da jikinsu zai rika samar da ƙwan kuma su kasa ɗaukar ciki.
Akan cire ƙwayayen daga jikin mace sai a daskarar da su sannan idan ta shirya ɗaukar ciki a fito da su, su saki sannan a yi mata dashensu a mahaifarta.
Damar mace ta ɗaukar ciki na raguwa yayin da take ƙara tsufa saboda inganci da yawan ƙwayayen halittarta na raguwa.
Daskarar da ƙwanta wani yunƙuri ne na adana damarta ta haihuwa ta hanyar daskarar da ƙwan a lokacin da mace take da kuriciyarta kuma ƙwayayenta ke da inganci sosai.
Ya ake daskarar da ƙwan?
Da farko, za a fara yi wa mace gwaji a tabbatar ba ta ɗauke da wata cuta kamar HIV ko ciwon hanta na Hepatitis. Gwajin ba zai shafi yiwuwar daskarar da ƙwan ko rashinsa ba, illa sai don a tabbatar an ware ƙwan da cutar ta shafa daga sauran lafiyayyu.
Daga nan sai a fara bin matakan inganta ƙwayayen - wannan kan ɗauki mako biyu zuwa uku kuma a kan bai wa mace magungunan da za su ƙara yawan ƙwayayenta kuma su taimaka masu su riƙa. Daga nan sai a ciro su daga jikin macen bayan an yi mata allurar bacci.
Bayan ciro ƙwan ana zuba shi a cikin wani sinadari don ya adana shi kuma ya kare shi daga abubuwan da ka yi masa illa.
Daga nan sai a daskarar da ƙwan ta hanyar sanyaya su sannan a zuba su a cikin wani wuri mai cike da sinadarin ruwan nitrogen.
Ana iya adana su tsawon shekaru goma wanda bayan nan ba a iya amfani da su wajen yin dashe, sai dai a zubar.
Idan mace ta yanke shawarar ɗaukar ciki ta hanyar amfani da ƙwayayenta da aka adana mata, sai a ciro su daga ma'adanarsu a bari su sake sannan a ƙyanƙyashen ƙwan a ɗakin gwaji, daga nan sai a dasa ɗan tayin a mahaifarta.
Me ya sa ake adana ƙwan mace?
Daskarar da ƙwai zaɓi ne ga matan da ba su shirya haihuwa ba a gaɓar da suke amma suna so su tabbatar da cewa sun yi tanadin haihuwar nan gaba.
Haka kuma, wasu na yanke shawarar yin hakan ne idan mace tana da wata cuta da ke shafar lafiyarta ta ɗaukar ciki.
Wannan na iya nufin cutar sikila ko cutar lupus da dai sauransu ko kuma idan mace na fama da cutar daji kuma ana yi mata gashin chemotherapy.
Akwai matsaloli?
Likitoci sun ce akwai bukatar mata sun san wasu abubuwa kafin su ɗauki matakin daskarar da ƙwayayensu:
- Ba lallai ne ƙwayayen su haifar da ɗa ba. Wato ana iya daskarar da su kuma idan aka fito da su daga ma'adanarsu, su gaza ƙyanƙyashewa.
- Babu tsayayyun shekaru da aka ware don adana ƙwayaye amma an fi so mace ta yi tsakanin shekarun 20 zuwa 30. Sai dai likitoci sun ce wannan ba ya nufin idan ta haura waɗannan shekarun ba za ta iya yi ba.
- Akwai wasu matsaloli da ka iya tasowa wajen fitar da ƙwayayen. Saboda magungunan da ake don inganta lafiya ƙwayayen, mace na iya fuskantar ciwon mara kuma fitar da ƙwayayen na da zafi ƙalilan. Haka kuma magungunan kan sa mace ta shiga halin yau farin ciki gobe takaici. Sai dai duka waɗannan matsalolin ba sa daɗewa, na wucin gadi ne.
- Matakan daskarar da ƙwan na da tsada, haka kuma kuɗin adana ƙwayayen ma na da matuƙar tsada. Don haka masu son adana ƙwan su tabbatar sua da isassun kuɗin biya.