Afghanistan: Harin ƙunar baƙin wake ya hallaka mutum 50 a masallaci a Kunduz

Asalin hoton, Getty Images
Wani mai ƙunar baƙin wake ya auka wa wani masallaci a birnin Kunduz na Afghanistan inda ya kashe aƙalla mutum 50 wanda hukumomi suka ce shi ne hari mafi muni tun bayan ficewar dakarun Amurka daga ƙasar.
An ga gawarwaki a baje a cikin masallacin na Said Abad wanda Musulmi ƴan Shi'a da basu fiye yawa ba ke amfani da shi.
Sama da mutum 100 ne suka jikkata a fashewar a birnin da ke arewaci.
Babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin, amma masu tsattsauran ra'ayin addinin Musulunci ciki har da ƙungiyar IS sun taɓa yunƙurin kai wa mabiya Shi'a hari.
Suna yi wa Musulmi ƴan Shi'a kallon waɗanda ba sahihan Musulmi ba.
IS-K, ɓangaren ƙungiyar IS na yankin Afghanistan wanda ke matuƙar adawa da Taliban, ya ƙaddamar da hare-haren bom da dama a baya-bayan nan musamman a gabashin ƙasar.

Asalin hoton, EPA
Zalmai Alokzai, wani ɗan kasuwa da ya gaggauta zuwa asibiti don ganin ko likitoci na buƙatar gudumowar jini, ya shaida halin rikicewar da asibitin ke ciki bayan harin na lokacin sallar Juma'ar.
"Motocin ɗaukar marasa lafiya na ta kaiwa da komowa don ɗaukar gawarwaki," ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Kafar yaɗa labarai ta Tolo News ta ruwaito hukumomi a yankin suna cewa sama da mutum 300 ne ke halartar sallar Juma'a lokacin da harin ya faru.

Babbar barazana ga ƙungiyar Taliban
Sharhi daga Secunder Kermani, wakilin BBC a Pakistan
Yayin da kawo yanzu babu ƙungiyar da ta ɗauki alhakin kai harin, wannan harin da duka alamu na ƙungiyar IS-K ne, ƙungiyar da ta kai hari filin jirgin sama na Kabul a watan Agusta.
Ƙungiyar ta sha yunƙurin kai wa ƴan Shi'a a Afghanistan hari, inda masu ƙunar baƙin wake ke kai hari masallatai da cibiyoyin wasannin motsa jiki da makarantu. A makonnin baya-bayan nan, IS ta ƙarfafa hare-harenta kan Taliban.
IS ta kai hari a lokacin wata sallar jana'iza da wasu manyan shugabannin Taliban suka halarta a Kabul ranar Lahadi, kuma sun kai ƙananan hare-hare a lardunan gabashi na Nangarhar da Kunar inda a baya IS ke da ƙarfin iko.
Harin na ranar Juma's, idan har IS ce ta kai shi, zai tabbatar da faɗaɗa ayyukansu a arewacin ƙasar.
Ƙungiyar Taliban ta ce ta kama gwamman mabobin IS kuma ana tunanin sun kashe wasu da ake zargi da alaƙa da ƙungiyar amma a zahiri ba su ɗauki barazanar da Is ke da ita a kansu ba da muhimmanci.
Ƴan Afghanistan da dama na fatan karɓe mulkin da Taliban ta yi zai buɗe wani sabon babi na zaman lafiya ko da kuwa za su zama masu kama karya.
Sai dai IS wata babbar barazana ce ga alƙawarin Taliban na inganta tsaro.

Ƙungiyar Taliban ta ƙwace iko da Afghanistan yayin da dakarun ƙasashen waje suka janye daga ƙasar a watan Agusta bayan yarjejeniya tsakanin Amurka da Taliban, shekaru 20 bayan da Amurkar ta cire ƴan bindigar daga mulki a shekarar 2001.










