Afghanistan: An bude babin sabon salon shugabanci a karkashin mulkin Taliban

Taliban spokesman Zabihullah Mujahid announcing the new government

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mai magana da yawun Taliban Zabihullah Mujahid ya saar da kafa sabuwar gwamnati a wani taron manema labarai a ranar Talata
    • Marubuci, Daga Lyse Doucet
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Chief international correspondent

A baya-bayan nan kalaman da ke fitowa daga 'yan Taliban sun sauya sosai ba kamar yadda aka saba ji ba a baya.

"Muna aiki don tabbatar da gwamnatin da za ta tafi da kowa da kowa wacce za ta wakilci al'ummar Afghanistan," kamar yadda daya daga cikin shugabannin Taliban Mullah Abdul Ghani Baradar ya fada a yayin da ya kai ziyara Kabul don fara tattaunawa kan tsarin shugabancin kungiyar, wanda zai fitar da ita daga masu yawo da bindigogi zuwa sahihiyar gwamnati.

"Muna son zama lafiya," a alkwarin da mai magana da yawun Taliban Zabihullah Mujahid ya yi, a taron manema labarai na farko a babban birnin kasar, bayan da Taliban ta kwace iko da gwamnati ranar 15 ga Agusta. "Ba ma son samun makiya na cikin gida da na waje."

Ku kalle su ta fuskar abubuwan da suke yi ba abubuwan da suke fada ba, su ne kalaman da suka fi yaduwa daga bakunan masu sanya ido kan Taliban da suka hada da 'yan kasar da gwamnatocin kasashen waje, da shugabannin kungiyoyin agaji da masu sharhi kan al'amuran siyasa a fadin duniya.

Amma 'yan Afghanistan suna sanya ido sosai kan dukkan abubuwan da ke faruwa. Dole ne su yi hakan.

A ranar da masu zanga-zanga rike da manyan kyallayen da aka yi rubuce-rubuce suka kwarara a kan titunan Kabul da sauran manyan birane - matan Afghanistan da ke jagorantar sauyin sun nemi a ba su 'yancinsu a ba su wakilci da ba su damar rawar da za su taka a cikin al'umma - a ranar ne kuma aka kaddamar da tsarin sabuwar gwamnatin Taliban.

Ko wannan hujja ce da ke nuna zakuwar Taliban ta son al'amuran yada labarai? A cikin lokacin kankani kanun labaran duniya suka manta da batun yadda suke harbe-harbe a iska da amfani da bakin bindiga da sanduna wajen tarwatsa masu zanga-zanga.

Amma an yi kwarya-kwaryar biki na yin taron manema labarai don isar da sako mai matukar muhimmanci da ake ta sauraro. Hakan ya faranta wa shafukan sada zumunta, sannan ya bakanta wa wadanda suka riki alkawuran Taliban da amana.

Maimakon zama gwamnatin da za ta tafi da kowa da kowa, sai ta zamo gwamnatin Taliban da ta ware wadansu. Tsohon tsarin gwagwarmayar Taliban, da hukumominta da mataimakanta, da kuma shugabanta mai cikakken iko Hibatullah Akhundzada, duk an sanya su a cikin majalisar zartarwar mai tsarin dimokradiyya irin ta kowace gwamntai a duniya.

An dawo da Ma'aikatar Tabbatar da Tsauraran Dokoki da aka sha sukarta a baya; sannan an rufe Ma'aikatar Harkokin Mata. Mafi yawan 'yan sabuwar gwamnatin 'yan kabilar Pashtun, sai mutum daya daga Tajik da daya daga Hazara dukkansu daga kabilar Talib.

Babu mace ko daya a sabuwar gwamnatin, ko da kuwa na mukamin mataimakan ministoci.

Gwamnati ce ta tsofaffin mayakan kungiyar, da kuma sabbin malamai wato mullah da kwamandojin soji: mazan da ke da iko a lokacin da Taliban ta yi mulki a shekarun 1990 wadanda suka dawo da dokar tsayar da gemu; da tsofaffin fursunonin gidan yarin Guantanamo; da wasu wadanda a yanzu haka suke cikin jerin masu laifin da Amurka da Majalisar Dinkin Duniya suka lissafa; da dakarun da ke yaki sosai a filin daga wadanda suka yi kokari sosai a watannin baya-bayan nan; da masu kokarin kyautata zaman lafiya da aka yi zaman sulhu da su da suka dinga zuwa wasu kasashen duniya da alkawuran kafa sabuwar Taliban ma cike da sauyi wato 2.0.

Taliban soldiers stand in front of protesters during the anti-Pakistan protest in Kabul

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mayakan Taliban na tsaye a gaban masu zanga-zanga a Kabul

Wasu sunayen an san su - wasu ga alamu za su iya zama masu saurin hasala.

Shugaban riko shi ne farin mutumin nan mai gemu Mullah Hasan Akhund, wanda shi ne ya kafa kungiyar Taliban da ke cikin jerin mutanen da Majalisar Dinkin Duniya ta sanya wa takunkumi.

Ministan da ke rikon kwarya a ma'aikatar harkokin cikin gida shi ne Sirajuddin Haqqani. Ba a faye ganin fuskarsa ba sai dai a hoto, ko a hakan ma wani mayani da ya lulluba ya rufe rabin fuskarsa, a jikin wani hoto da FBI ta wallafa na mutanen da take nema ruwa a jallo da alkawarin ba da tukwuicin dala miliyan biyar ga wanda ya samo shi.

Ana zargin kungiyar Haqqani da ke da sunan zuri'arsa da kai munanan hare-hare a kan fararen hular Afghanistan. Sai dai 'yan zuri'ar Haqqani sun dage cewa babu wannan kungiyar, kuma yanzu suna cikin Taliban ne.

Ministan Tsaro na rikon kwarya shi ne Mullah Yaqoob, babu hotonsa, kuma shi ne babban dan wanda ya kirkiri kungiyar Taliban wato Mullah Omar.

Amma, dan jira, wannan majalisar wucin gadi ce kawai.

A taron manema labaran na Kabul, a lokacin da 'yan jarida ke karadin yin tambayoyi, an ce za a sanar da wasu mukaman nan kusa.

"Ba mu kammala sanar da dukkan ma'aikatun da mataimakansu ba tukunna, don haka akwai yiwuwar za a kara yawan shugabannin," in ji Ahmadullah Wasiq, mataimakin hukumar al'adu, kamar yadda ya shaida wa abokin aikina.

Wannan na iya kasancewa mafarin romon dimokradiyya na saka wa mayakan kan irin gwagwarmayarsu, wadanda da yawansu suke ta kwarara Kabul, don yin maraba da dawowar "tsarin shari'ar Musulunci"

Hakan ya nuna kamar dama wani abu ne tsararrre na ban gishiri in ba ka manda. A wani yanayi na ba-zata sai Mullah Akhund ya zama shugaba, wanda hakan ya sasanta adawar siyasa da ta kabilanci da suka hada da Mullah Baradar, wanda mutane da yawa suka yi hasashen shi ne zai zama shugaban, maimakon kujerar mataimakin shugaba.

1px transparent line

An ce shugabannin Taliban sun ki yarda da sanya jagororin siyasa na baya a tafiyar tasu, musamman wadanda aka yi wa shaidar cin hanci, suna masu cewa sun ci zamaninsu a baya.

Har yanzu wasu kalmomi na kururuwa a kunnena wadanda suka fito daga bakin mai sasanci na Taliban Sher Mohammad Abbas Stanikzai, wanda a yanzu aka nada shi a matsayin mataimakin ministan harkokin kasashen waje, irin mukamin da ya rike a wancan karon.

A lokacin da na tambaye shi a watan Fabrairun 2020, bayan cimma yarjejeniya tsakanin Amurka da Taliban, kan ko me zai cewa 'yan Afghanistan da ke tsoron komawarsu, sai ya mayar da martani cikin azama da cewa: "Na gaya musu cewa za mu kafa gwamnatin da mafi yawan mutane za su yi maraba da ita." A lokacin da ya zo fure "mafi yawa" din sai da ya jaddada tare da kaurara murya.

Wato dai, gwamnatin da aka mamaye ta da dokokin al'adu, ba irin dokokin da suke gwasalewa ba a matsayin na kasashen yamma.

Tsarin mulkin Taliban

Shekara daya bayan nan, a ranar farko ta tattaunawar cimma yarjejeniyar da Afghanistan a Qatar, an yi shewa a dakin taron lokacin da Taliban ta ba da haske cewa ba za ta bukaci kafa Daular Musulunci ba; suna masu cewa sun gane damuwar da ake da ita a kanta.

A tattaunawarsu da mata masu sasanci kuwa, sun tabbatar musu da cewa mata za su iya taka kowace rawa ban da zama shugaban kasa, ciki har da ma'aikatun gwamnati.

A da kenan. Yanzu ana maganar yanzu ne. Taliban ne ke da karfin iko.

"Wadanda ba su mayar da hankali kan zamantakewar Afghanistan ba za su fuskanci kalubale," kamar yadda mai shiga tsakani Fawzia Koofi, ta yi gargadi.

Tuni dai aka fara ganin kalubalen a zanga-zangar da ake yi a kan tituna, kamar yadda yake kunshe a sanarwar kasashen duniya da dama.

Kuma wani kalubalen ma zai iya bullowa ne daga cikin matasa masu tasowa.

Taliban stand guard outside the building of former US embassy as the wall painted with text in Arabic "There is not God but Allah, Muhammad is the messenger of Allah" in Kabul

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani mayakin Taliban na tsaye a gaban ginin tsohon ofishin jakadancin Amurka

A wata sanarwa da aka fitar jim kadan bayan sanar da tsarin shugabancin rikon, sarkin ya nuna cewa ana neman kwararrun mutane masu basira ido rufe don a yi aiki da su.

Amma dai idan aka duba, za a ga cewa so ake a karfafa tsarin shari'ar Musulunci da sake kafa ta a kasar.

A kwanakin baya-bayan nan a Kabul, na tambayi masu sa ido kan Taliban daga bangarori daban-daban kan mene ne tunaninsu kan tsarin shugabancin Taliban, ko zai zama mai tsauri ko me sassauci a nan gaba.