An rufe gidan talbijin saboda mai gabatar da shirye-shirye ya yi waka

Asalin hoton, AFP VIA GETTY IMAGES
Hukumomin Tunisiya sun rufe wani gidan talbijin, bayan daya daga cikin masu gabatar da shirye-shiryensa ya karanta wata rubutacciyar waka ta kin jinin shugaba dan kama-karya.An kama tare da zargin Amer Ayad - mai gabatar da wani shirin tattaunawa a gidan Talbijin din na Zitouna, da yin zagon kasa ga harkokin tsaron Tunisiya.Gidan talbijin d'in Zitouna ya rika sukar lamirin dakatar da majalisar dokokin kasar da Shugaba Kais Saied, ya yi kwanakin baya, da kuma kwace kusan dukkan harkokin mulki a kasar.Hukumomin kasar sun ce tashar tana aiki ne ba bisa ka'ida ba.Uganda : Yadda sojoji suka lakaɗawa ƴan jarida duka
A ranar 3 ga watan Satumbar, 2021 ne, Amer Ayad, ya karanta rubutacciyar wakar da ake kira da suna The Ruler, wato Shugaba ta Ahmed Matar a kafar yada labaran.
Ahmed Matar ya shahara da rubutattun wakokinsa na shagube da sukar lamirin masu mulkin kama-karya a kasashen Larabawa. An kama Amer Ayad ba da dadewa ba.
Kamen na sa shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin kamen da aka yi wa 'yan jarida da kuma 'yan majalisu wadanda suka nuna rashin amincewarsu da matakan shugaban kasa.
A ranar Laraba, wato 6 ga watan Satumbar, 2021, gidan talbijin din na Zitaouna ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, jami'an tsaro sun afkawa dakunan watsa shirye-shiryensa tare da lalata kayan aikin da ke ciki.
Wani babban jami'i a gwamnatin kasar Nouri Lajmi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, gidan talbijin din na Zitaouna ya shafe shekaru yana aiki ba bisa ka'ida ba.
A shekarar 2012, Zitouna ya fara watsa shirye-shiryensa, bayan faduwar gwamnatin Zine al-Abidine Ben Ali, ta jima kan mulki a kasar.
A shekarar 2015, an kwace wasu daga cikin kayan aikin gidan talbijin din Zitouna, amma kuma ya ci gaba da aiki a haka.











