Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lars Vilks: Mota ta hallaka wanda ya yi zanen ɓatancin Annabi Muhammadu a Sweden
Wani ɗan ƙasar Sweden da ya yi zanen ɓatancin Annabi Muhammadu ta hanyar zana abin da ya kiran kan Manzon Allah a kan gangar jikin kare ya mutu a wani hatsarin mota, a cewar kafafen yaɗa labaran ƙasar.
Rahotanni sun ce Lars Vilks yana tafiya ne a cikin wata motar ƴan sanda marar fenti wacce ta yi taho mu gama da wata babbar mota a kusa da garin Markaryd da ke kudancin Sweden.
Wasu jami'an ƴan sanda biyu ma sun rasa rayukansu sannan direban babbar motar ya jikkata.
Vilks mai shekara 75 yana ƙarƙashin kulawar ƴan sanda sakamakon barazanar da ya yi ta fuskanta bayan yin zanen ɓatancin.
Zanen wanda aka wallafa a shekarar 2007, ya harzuƙa Musulmai da dama wadanda suke ganin duk wani zane da za a yi na fiyayyen halittar saɓo ne. Ya yi zanen ne shekara ɗaya bayan da wata jaridar ƙasar Denmark ta wallafa zane-zanen Manzon Allah.
Ƴan sanda ba su bayyana sunayen wadanda suka mutu a hatsarin na ranar Lahadi ba, amma budurwar Vilk ta tabbatar da mutuwar tasa ga jaridar Dagens Nyheter.
Wata sanarwa daga ƴan sanda ta ce har yanzu ba a san yadda hatsarin ya faru ba amma dai alamu sun nuna ba wani ne ya kitsa shi ba.
Zanen ɓatancin ya jawo tashin hankali har sai da firaministan ƙasar na wancan lokacin Fredrik Reinfeldt ya gana da jakadu 22 na ƙasashen Musulmai, a wani ƙoƙari na yayyafa wa lamarin ruwan sanyi.
Jim kaɗan bayan hakan ne, ƙungiyar al-Qaeda da ke Iraƙi ta sanya tukwicin dala 100,000 ga duk wanda ya kashe shi.
A shekarar 2015, Vilks ya halarci wata muhawara kan ƴancin faɗin albarkacin baki inda aka kai harin bindiga a birnin Copenhagen. Ya ce mai yiwuwa shi aka so kashewa a harin, wanda ya yi sanadin mutuwar wani daraktan fim.
Wa tana Yunin 2021 ma mai zanen shaguben nan a jarida dan kasar Denmark Kurt Westergaard, wanda aka fi saninsa saboda zanen da ya yi na Annabi Muhammad (SAW) wanda ya janyo ce-ce-ku-ce, ya mutu.
Ya mutu yana da shekarun 84 bayn ya sha fama da jinya, kamar yadda iyalansa suka shaida wa jaridar Berlingske.