Muna cikin kunci saboda rashin zuwa makaranta - Wasu dalibai a Kano

Kano

Ɓangaren ilimi a Najeriya na daya daga cikin inda ake fuskantar matsaloli musamman a arewacin kasar da aka bayyana ke kan gaba wajen adadin yaran da basa zuwa makaranta.

Lalacewar dakunan karatu ne na farko, baya ga rashin kulawa da hakkokin malaman da ya kamata a ce sun samu karfin guiwar aikin su, na koyarwa don samun ingantaccen ilimi wa yaran.

Matsalolin dai na yin mummunan tasiri ga yanayin daukar darussa a bangaren daliban da su kansu malaman.

Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriyar na ɗaya daga cikin jihohin da ake fama da irin wadannan matsaloli na lalacewar makarantu da kuma tilastawa wasu daga cikin daliban karatun hakura da karatu, duk kuwa da shirin gina sabbin gine-gine biyu a kananan hukumomin jihar 44.

'Karatunmu na cikin barazana'

Halin da makaranatar Sakandaren Kogo a karamar hukumar Kiru ke ciki
Bayanan hoto, Halin da makaranatar Sakandaren Kogo a karamar hukumar Kiru ke ciki

Wata makarantar sakandare da ke garin Kogo a yankin karamar hukumar Kiru a jihar Kano wacce ta maza da mata ce, na da dakunan karatu takwas amma kuma yanzu babu ko da dalibi guda a ciki.

Yau shekara biyu kenan da aka ba su aron dakunan karatu hudu a wata makarantar firamare inda malamai ke ci gaba da koyar da daliban a cikin hali na kuntata.

Ɗaya daga cikin daliban wannan makaranta mai kimanin shekara 15 ya shaida wa BBC cewa sun baro makarantar ta su saboda iska da ya yaye rufin dakunan karatun, kana bangwayen sun tsattsage.

"Yanzu dai kam karatu gashi nan muna yi, mun zo mun roka inda aka ba mu azuzuwa wanda za mu samu inda za mu tsuguna mu yi karatu kafin Allah ya sa mu samu wanda zai zo ya gyara mana," in ji dalibin.

Ya kuma kara da cewa: "Azuzuwan sun yi mana kadan gaskiya, kuma hayaniya da surutai daga 'yan makarantar firamare da ke kusa, da kuma jama'ar gari da ke wucewa, hakan na shafar karatunmu."

Shekara guda kenan da iska ya yaye rufin makarantar
Bayanan hoto, Shekara guda kenan da iska ya yaye rufin makarantar

Ita ma wata daliba ta bayyana wa BBC cewa tana rokon da a kawo musu dauki saboda karatunsu da makomar iliminsu na fuskantar barazanar yiwuwar tabarbarewa.

"Kusan shekara biyu kenan muke ta fama a nan, hakan gaskiya na shafar karatunmu, a baya lokacin da nake zuwa makaranta babu nisa da gidanmu amma yanzu sai mun yi tafiya mai nisa kafin mu zo nan," a cewarta.

Dalibar ta kuma ce tana da burin nan gaba idan ta samu nasarar kammala karatu ta zama likita, sai dai kuma ta ce dole sai an tallafawa karatun nasu saboda ba sa gane darasin da malamin ke koyarwa saboda cunkoso a dakunan karatun.

"Azuzuwanmu a cunkushe suke ga kuma hayaniya daga waje, don haka ba ma iya jin abubuwan da ake fada, don haka ba ma iya gane komai."

Daliban makarantar da dama na kokawa da cewa muddin gwamnati ba ta kawo musu dauki ba, makomar karatun na su za ta lalace.

Ɗaya daga cikin malaman makarantar ya shaida wa BBC cewa sun kai kusan shekara biyu suna gudanar da karatu a wurin da aka ba su aron azuzuwa hudu a wata makarantar firamare.

Dalibai ba sa iya daukan darussa a wadanan azuzuwa saboda damina
Bayanan hoto, Dalibai ba sa iya daukan darussa a wadanan azuzuwa saboda damina

"Da muna da dalibai kimanin dari uku, yanzu nan wurin ya yi mana kadan, ba zai iya daukar addadin daliban da muke da su ba, hakan yana shafar zuwan su kan su daliban makaranta," in ji malamin.

Shi ma ɗaya daga cikin iyayen daliban wannan makaranta ya nuna damuwarsa game da halin da 'yayansu ke ciki game da karatun.

"Ya kamata gwamnati ta kawo dauki, kowa ba ka rasa shi da burinsa na abinda yake so ya zama a nan gaba, yanzu da za ka tambayi daliban ɗaya bayan ɗaya za ka tarar suna da burin zama wani abu," in ji shi.

Me gwamnatin Kano ke cewa?

Kano

Asalin hoton, KNSGV

Hukumomin da abin ya shafa a jihar Kanon sun ce suna sane da wannan matsala kuma suna shirin daukar matakai.

Kwamishinan Ilimi na jihar Kano Sanusi Sa'idu Kiru ya bayyana wa BBC cewa yanzu haka suna nan suna shirin daukar matakai na duba yadda za a gyara makarantar da ma sauran makarantun da suka lalace a jihar.

"Bai fi mako biyu ba da al'ummar wannan gari suka zo suka kawo korafinsu kuma muka tura aka duba wannan makaranta aka kuma yi kiyasi na abinda ake bukata domin a gyara makarantar," in ji kwamishinan.

"Don haka muna jiran abin da aka yi kididdiga sannan za mu tura gaba don neman amincewar gwamnati, kafin nan a fara gyara wannan makaranta.''