Ko ina aka boye fursunonin siyasar Eritrea shekaru 20 baya?

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International na gangamin matsawa gwamnatin Eritrea lambar bayyana inda suka kai fursunonin siyasa 21 da aka kama shekaru 20 da suka gabata.

A watan Satumbar 2001 ne gwamnati ta rufe kafar yada labaran Eritrea mai zaman kan ta, tare da kame 'yan siyasa 11, wadanda suke sukar lamirin shugaba Isaias Afewerki, an kuma kame 'yan jarida 10 da suka wallafa makalar a gidajen jaridar da suke yi wa aiki.

Gwamnati ta ce wadanda ta kama din su na barazana ga tsaron kasa. Ba dai a taba gurfanar da mutanen gaban shari'a ba, sannan ba bu wanda ya san inda ake tsare da su.

Eritrea dai ba ta gudanar da zabe ba, tun bayan samun 'yancin kai a shekarar 1993, sannan shugaba Isaias ba jagorantar kasar kusan shekaru 28 kenan.

Amnesty bada bayanin mummunan yanayin da gidajen kason kasar ke ciki, a wasu lokutan ana samun bayanan cin zarafi da musgunawa fursunoni.

'Yan Eritrea mazauna kasashen waje, da 'yan uwan fursunoni siyasar da ake tsare da su na shirin shirya gagarumin taro a kasashen duniya nan da shekara daya, domin jan hankalin duniya don sanin halin da ake ciki.

A shekarar 2022 za su gabatar da makala a majalisar gwamnatin Birtaniya da ke birnin Landan , da majalisar Scotland da ke Edinburgh da wasu rassan ofishin kungiyar Amnesty International.

Tuni Amnesty ta fara wani kamfe a shafin Twitter, inda aka kirkiro maudu'in #WhereAreEritreasDissidents?, tare da fatan samun wani bayani da zai haska hanya gano halin da mutanen ke ciki, ko a mace ko a raye.