Kun san wurare shida a duniya da rana ba ta faɗuwa sama da kwana 70?

Sun setting behind Manstone Rock

Asalin hoton, Andrew Fusek Peters

Ka yi tunanin yadda masu yawon buɗe ido za su ji a wurin da ba a ganin rana tsawon kwana 70 a jere, alhali su ma mazauna yankin da kansu a rikice suke game da rashin ranar.

Rayuwarmu ta dogara ne kan sa'o'i 24 a rana, sa'o'i 12 a wuni guda, sauran sa'o'in kuma dare ne.

Sai dai me? Shin kun san cewa akwai wurare a duniya da rana ba ta faɗuwa fiye da kwana 70?

Ga wurare shida a duniya inda rana ba ta faɗuwa.

Norway

Norway, wacce ke cikin Arctic Circle, ana kiranta 'Land of the Midnight Sun,' inda daga watan Mayu zuwa ƙarshen Yuli, rana ba ta faɗuwa.

Wannan yana nufin cewa tsawon kusan kwanaki 76, rana ba ta faɗuwa.

A yankin Svalbard na Norway, rana tana haskawa daga 10 ga Afrilu zuwa 23 ga Agusta.

Haka nan yanki ne na Arewacin Turai.

Kuna iya shirya kai ziyara wannan wuri a wannan lokacin kuma ku zauna tsawon kwanaki ba tare da kun ga dare ba.

Nunavut, Canada

Woman sitting on a balcony at sunset

Asalin hoton, Getty Images

Yankin Nunavut yana kusa da Arctic Circle, a sassan Arewa maso Yammacin Canada.

Wannan wurin na ganin hasken rana kusan tsawon watanni biyu kowace rana, yayin da lokacin hunturu, wurin yana ganin kusan kwanaki 30 a jere na duhu gaba ɗaya, wato rana ba ta fitowa.

Iceland

Iceland shi ne tsibiri mafi girma a Turai bayan Birtaniya, kuma kasa ce da babu sauro.

A lokacin bazara, dare ba ya yi a Iceland wato babu duhu gaɓa ɗaya, kuma a watan Yuni, rana ba ta faɗuwa.

Don ganin rana da tsakar dare a zahirinta, za ku iya ziyartar garin Akureyri da Grimsey Island a cikin Arctic Circle.

Barrow, Alaska

A bright sun in an intensely orange sky

Asalin hoton, Getty Images

Daga ƙarshen watan Mayu zuwa ƙarshen Yuli, rana ba ta faɗuwa a nan, sai a farkon Nuwamba inda take kwanaki 30 ba ta fito ba, kuma an fi sanin wannan yanayin da 'polar night'.

Wannan na nufin cewa ƙasar na kasancewa cikin duhu a lokacin hunturu.

Haka kuma yankin ya yi suna da tsaunukansa da ke lulluɓe da dusar ƙanƙara. Ana iya ziyartar wannan wuri a lokacin bazara ko hunturu.

Finland

Ƙasa mai dubban tabkuna da tsibirai, ɓangarori da yawa na Finland suna samun hasken rana kai tsaye na kwanaki 73 kawai a lokacin bazara.

A lokaci guda kuma, rana tana ci gaba da haskawa tsawon kusan kwanaki 73, yayin da a lokacin hunturu, yankin ba ya ganin hasken rana kwata-kwata.

Hakan na ɗaya daga cikin dalilan da suka sa mutane ba sa bacci sosai a lokacin bazara, kuma fiye da haka lokacin hunturu.

Yayin da kuke nan, za ku samu damar ganin 'Northern Lights', wani haske mai walwali da ake iya gani a nan kuma za ku samu damar yin tseren ƙankara.

Sweden

Daga farkon watan Mayu zuwa ƙarshen watan Agusta, Sweden tana ganin faɗuwar rana da tsakar dare da tashinta da misalin ƙarfe 10 na safe.

A nan, ana iya jera wata shida ana kusufin rana.

Don haka yayin da kuke nan, mutum na iya kashe lokacinsa yana wasan golf da kamun kifi da tafiye-tafiye, da dai sauransu.