Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Aisha Buhari ta yi karin haske kan bidiyon Pantami da ta wallafa
Uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari ta yi karin haske a kan wani bidiyo na wa'azin Ministan Sadarwar kasar, kuma malamin Islama Sheikh Isa Ali Pantami, da ya nuna shi yana kuka bayan karanta wata ayar Al-Kur'ani da mai jan bakinsa ya yi a wajen tafsiri.
A ranar Lahadi ne Aisha Buhari ta wallafa bidiyon da gajeren sako da ke cewa "Tunatarwa: A cire tsoro a yi abin da ya dace."
Wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce a kasar inda mutane suke fassara shi da manufofi daban-daban, wasu na ganin shagube take yi wa Pantamin da ganin rashin kyautawarta kan hakan, yayin da wasu kuma ke ganin ta kyau idan ma shaguben ta yi.
Amma a ranar Litinin sai Uwargidan Shugaban Kasar ta sake wallafa bidiyon da sakon da ya fi na farko tsayi, inda take cewa: "Tafsir na Malam kan tsoron Allah ba tsoron mutum ba!
"Da aka cire tsoro da son Kai aka shiga Jihar Zamfara, abubuwa sun fara kyau. Sai a dage a shigo sauran wurare da ke bukatan haka."
Wannan sakon na baya kai tsaye ya fassara abin da Hajiya Aisha take nufi da sakon farkon wanda mutane suka dinga ba shi fassara daban-daban.
Sakon Aisha Buhari na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke cikin wani yanayi na rashin tsaro a sassan kasar daban-daban, da suka hada da matsalar 'yan bindiga a arewa maso yammacin kasar, inda ake yawan satar dalibai daga makarantu.
Kazalika 'yan bindigar na yawan kai hare-hare kan kauyuka da kashe mutane da sace don karbar kudin fansa. 'Yan Najeriya sun yi ta harzuka da nuna fushi kan rashin daukar wasu matakan a zo a gani don dakile wadannan matsaloli.
Sai dai a baya-bayan nan gwamnatocin jihohin da abin ya shafa da na gwamnatin tarayya sun sake fitar da wasu sabbin matakan da suka hada da katse layuakn waya a Jihar Zamfara da wasu sassan jihar Katsina, tare da kai hare-haren sama da jiragen yakin soji kan maboyar 'yan bindigar da ke dazuzzukan yankin.
Don haka kai tsaye sakon Aisha Buhari na biyu yana magana ne a kan wannan matsala, wacce take faruwa karkashin gwamnatin mijinta.
Sai dai yin tsokacin nata ba abin mamaki ba ne don ba shi ne karo na farko da Aisha Buhari ta taba sukar lamirin maigidan nata ba.
Karin labarai masu alaka
Kalaman Aisha Buhari na sukar lamirin gwamnatin mijinta
Tun lokacin da mijinta, Muhammadu Buhari ya karbi ragamar mulkin Najeriya, Aisha Buhari ke gabatar da 'yan korafe-korafenta kan gwamnatinsa.
Ma'ana, tana amayar da abin da ke ranta wanda bai mata dadi ba, musamman a kafafen sada zumunta kamar tuwita da instagram da dai sauransu.
Ga wasu daga cikin maganganunta da suka ta da kura:
- Buhari ya watsar da yawancin wadanda suka taimaka ya hau mulki.
- Rashin magani a asibitin fadar gwamnati.
- Rikicin cewa iyalan Mamman Daura sun rufe mata kofa.
- Korafi kan masu hana ruwa gudu.
- Korafi kan Garba Shehu.
- Rikicinta da Tunde Sabi'u.
- Kamfe dinta kan maudu'in 'A ceci jama'a'.
- Maganarta kan wa'azin Pantami.