Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Korafe-korafen Aisha Buhari guda 5 kan gwamnatin Buhari
Aisha Buhari ita ce uwar gidan shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari wadda ta yi fice kamar sauran takwarorinta da suka gabata.
Tun lokacin da mijinta, Muhammadu Buhari ya karbi ragamar mulkin Najeriya, Aisha Buhari ke gabatar da 'yan korafe-korafenta kan gwamnatinsa.
Ma'ana, tana amayar da abin da ke ranta wanda bai mata dadi ba, musamman a kafafen sada zumunta kamar tuwita da instagram da dai sauransu.
A kan me take korafi?
1. Buhari ya watsar da yawancin wadanda suka taimaka ya hau mulki.
A shekarar 2016, BBC ta yi wata kebantacciyar hira da Aisha Buhari, inda ta bayyana korafe-korafe da dama musamman a kan maigidanta Muhammadu Buhari.
A cikin hirar, mai dakin shugaban Najeriyar, ta bayyana cewa mijinta ya yi watsi da mafi yawancin wadanda suka taimaka masa ya hau mulki.
Aisha Buhari a cikin hirar ta ce, ''Wadanda ba su yi wahala ba; wadanda ko katin zabe ba su da shi su suka zauna a kan mutane suke yin komai da komai. Abin da nake guje musu (su manyan APC) shi ne boren da mutum miliyan 15 za su yi".
Wannan kalamai na mai dakin shugaban kasar sun jawo mata yabo da suka a wajen 'yan Najeriya.
2. Rashin magani a asibitin fadar gwamnati
A shekarar 2017, Aisha Buhari ta sake yin korafi a kan rashin magunguna a asibitin da ke fadar gwamnatin Najeriya.
Mai dakin shugaban kasar ta yi wannan korafi ne bayan da ta ziyarci a asibitin, inda ta ce ta tarar dai-dai da kwayar paracetamol babu a asibitin.
Aisha Buhari ta bayyana korafin nata ne a wajen wani taron masu ruwa da tsaki a kan lafiya, inda a nan ne take fadin cewa ga abin da ta tarar a asibitin fadar shugaban kasa, wanda haka a cewarta abin takaici ne duba da yadda ake ware wa bangaren lafiya makudan kudade.
Mai dakin shugaban kasar ta ce, a asibitin fadar shugaban kasa ma an rasa magani, ina ga sauran asibitocin gwamnati.
3. An rufe mata kofa
Wani korafi da Aisha Buhari kuma ta yi shi ne, a kan wani bidiyo ta aka rinka yadawa a kafafen sada zumunta wanda a cikinsa aka gan ta tana ta fada da harshen Turancin Ingilishi tana gaurayawa da Hausa.
Jama'a da dama a lokacin da suka ga bidiyon sun yayata cewa Aisha Buhari ce ta dawo daga Ingila tana fada cewa an rufe mata kofar daki.
To sai dai kuma a wancan lokacin Aisha Buhari, ta tabbatar wa BBC cewa ita ce aka dauka a cikin bidiyon amma ta ce tsohon bidiyo ne.
Fitowar hoton bidiyon da aka nada a boye ya zo a daidai lokacin da ake rade-radi a kafafen sada zumunta cewa shugaba Muhammadu Buhari zai auri ministarsa ta ayyukan agaji da kula da bala'i, Sadiya Umar Farouk.
Wannan batu ma ya ja hankali sosai, saboda a lokacin da ake ta yada jita-jitar, mai dakin shugaban kasar ba ta kasar. Hakan ya sa aka rinka cewa ta yi yaji, amma bayan dawowarta daga tafiyar da ta yi, Aisha Buhar ta yi watsi da jita-jitar da aka yi ta bazawa, inda ta ce ta tafi ne domin a duba lafiyarta sannan kuma ta samu lokaci da 'ya'yanta kamar yadda ta saba yi a duk shekara.
Sai dai a wata hira da ta yi da manema labarai jim kadan bayan saukarta, mai dakin shugaban kasar ta yi shagube ga wacce aka ce Buharin zai aura, inda ta ce ministar ba ta musanta batun auren ba sai da ranar auren ta wuce tukuna.
4. Masu hana ruwa gudu
Maganar cewa akwai wasu da suke hana ruwa gudu a gwamnatin Buhari na daga cikin korafe-korafen Aisha Buharin.
Mai dakin shugaban kasar ta ce ba dan wadannan mutanen da suka kankane gwamnatin mijin nata ba, da an samu ci gaban da ya fi wanda aka samu.
Ta ce su wadannan mutane da ba ta bayyana ko su wane ne ba, na hana ruwa gudu a gwamnatin.
Wannan korafin nata ma ya janyo ce-ce-kuce a kasar, inda aka yi ta yada kalaman nata a kafafen sada zumunta, ana kuma tofa albarkacin baki aka.
5. Garba Shehu
Sai kuma korafi na baya-bayan nan wanda ta zargi mai taimaka wa shugaban kasar a kan harkokin yada labarai Mallam Garba Shehu da zama dan koren wasu mutane a fadar gwamnati.
Hajiya Aisha Buhari ta ce sau da yawa ba ya tsayawa ya kare martabarta a lokutan da bukatar hakan kan taso.
Mai dakin shugaban kasar ta wallafa a shafinta na twitter da kuma wata sanarwa da ta fitar cewa, Garba Shehun, ya fi karkata wajen wasu da ta yi shagube tana bayyana su da cewa mutane ne masu farcen-susa ko ikon-boye a fadar shugaban kasar, duk da cewa ba zababbu ba ne, wadanda ta ce sukan yi shisshigi ga harkokin da suka shafi iyalan shugaban kasa.
Ta yi misali da wata dambarawar da aka yi a fadar shugaban kasar, wadda aka yada a wani hoton bidiyo, wanda a ciki aka nuna ta a wata kofar gida da ke fadar an rufe mata kofa, tana kumfar-baki tana neman mutanen da ke ciki, wadanda ta tabbatar da cewa iyalin dan`uwan shugaba Buhari, wato Maman Daura da su bude mata kofa! Labarin da Aisha Buhari ta ce an jirkita shi, amma Garba Shehu bai fito ya gyara maganar ba. Tana cewa wannan butulci ne.
Wadannan korafe-korafe dai da take yi dai wata alama ce da ke nuna yadda ake samun rashin jituwa tsakaninta wasu mukarraban shugaban na Najeriya.