Aisha Buhari: Na dawo daga jinya amma jirginmu ya samu matsala a hanya

Lokacin karatu: Minti 1

Mai ɗakin shugaban Najeriya Aisha Buhari ta ce jirgin da ya ɗauko ta domin dawo da ita gida daga jinyar da ta yi ya fuskanci matsala.

Sai dai ta ce matuƙa jirgin da ma'aikatansa sun nuna ƙwarewa da bajinta wurin sassaita shi.

Ta bayyana haka ne a saƙon da ta wallafa a shafinta na Twitter bayan komawar ta Najeriya daga jinyar da ta kwashe lokaci tana yi a ƙasar waje.

"Zan yi jinjina da kuma nuna jin daɗina game da jajircewa da ƙwarewa da direban jirgin da ma'aikatansa suka nuna, da kuma zaratan sojojin sama maza da mata na rundunar sojin sama na Najeriya kan aiki tuƙuru da suke yi wurin kula da jiragen rundunar," in ji ta.

Aisha Buharin dai ta bar Najeriya ne tun bayan Babbar Sallah inda wasu jaridun Najeriya suka ruwaito cewa ta tafi Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin neman magani.

Sai dai ko a saƙon da ta wallafa a shafinta na Twitter, sai da ta yi hannunka mai sanda ga ɓangaren kiwon lafiya na Najeriya inda ta ce ya kamata a ƙara inganta shi domin rage tafiye-tafiye zuwa ƙasashen ƙetare domin neman magani.

Ko a shekarun baya sai dai uwar gidan shugaban ƙasar ta yi tir da asibitin fadar shugaban ƙasar inda ta ce yana cikin wani hali