Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Auren Yusuf da Zahra: Yadda jiragen sama da attajirai suka kece raini a Bichi
Kananan jiragen da ba na fasinja ba sun cika filin jirgin saman Malam Aminu da ke birnin Kano a arewa maso yammacin Najeriya sakamakon halartar daurin auren ɗan shugaban kasa da 'yar sarkin Bichi da masu ido da kwalli daga sassan kasar da ma wasu kasashen Afirka suka yi.
Auren Yusuf Buhari da Zahra Nasir Bayero na daya daga cikin manyan shagulgulan da aka yi a bana a kasar.
Dubban mutane ne suka halarci Fadar Sarkin Bichi a jihar Kano.
Wani masanin tarihi ya shaida wa BBC cewa ba a faye yin aure a tsakanin iyalan gidan shugaban kasa da na gidajen sarauta ba a Najeriya.
Rahotanni sun ce sabbin ma'auratan sun hadu ne a Jami'ar Surrey a Birtaniya.
An ci gaba da shagulgulan biki a ranar Asabar, inda aka bai wa uban amaryar, Nasir Ado Bayero sandar girma ta tabbatar masa da Sarautar Bichi.
Yayansa shi ne Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.
Wasu labarai masu alaƙa
Sai dai amarya da ango su ba su halarci wannan hidimar ba.
Dangin ango sun ba da sadakin naira 500,000 - kudin da ya kai nunki 10 na matsakaicin abin da mafi yawan mutane ke iya mallaka a Najeriya.
Hotonan amarya da ango da suka yi gabanin auren sun jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda wasu suka ce shigar ba ta dace da addini ba saboda kafaɗunta a waje suke, amma wasu kuma sun kare ta.
Yayin da wasu rahotanni ke cewa jirage 100 ne suka sauka a Kano don kai baƙi, wani ma'aikacin filin jirgin saman ya shaida wa BBC cewa ba su fi 50 ba.
Sai dai duk da haka an rage kaifin shagulgulan saboda yaki da yaduwar cutar korona.
Mafi yawan mahalartan sun sanya takunkumi, saboda yadda Najeriya ke fama da dakile yaduwar cutar da ke sake bazuwa.
An tsaurara tsaro a wajen biki, inda 'yan sanda da sojoji suka mamaye fadar suna gadinta.
Ministan Sadarwa Isa Ali Pantami ne ya daura auren, a matsayinsa na babban malami.
Manyan 'yan siyasa da sarakunan gargajiya daga ko'ina a fadin kasar ne suka halarci daurin auren.
Daga cikinsu akwai Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo da tsohon Shugaba Kasa Goodluck Jonathan da kuma tsohon matamakin shugaban kasa kuma dan takarar shugabacin kasa na PDP a 2019 Atiku Abubakar.
Sannan tsohon shugaban kasar Jamhuriyyar Nijar ma Muhammadu Issoufu da kuma matar shugaban kasar Gambiya Fatoumata Bah Barrow duk sun samu halarta.
Biki, buduri bureɗe
Kowa ya san mata da biki, to su ma ba a bar su a baya ba.
A Kano dangin amraya sun yi yinin biki na al'ada da kamun amarya da kuma wata al'ada da ake kira lugude, a ranar Laraba a cikin Fadar Sarkin Kano, wato gidan wan mahaifin amarya.
An yi kide-kiden ƙwarya da gaɗa da sauran hidimomin al'ada. Sai dai an sanya matakan hana ɗaukar hotuna.
Wataƙila shi ya sa ba a ga bazuwarsu sosai ba.
Sannan ranar Juma'a bayan ɗaurin aure da daddare an yi liyafa a cikin birnin Kano. Mawaƙin da ake ya yi Hamisu Breaker ne ya gwangwaje a wajen taron.
Manyan mutane maza da mata sun samu halarta, amma duk da matakan hana ɗaukar hotuna, a wannan karon sai da aka samu abzuwarsu.
A ranar Asabar kuma aka kai amarya Fadar Shugaba Ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja, wato gidan surukanta.
Da yammacin ranar dangin ango suka yi mata buɗar kai kamar yadda ake yi a al'adar Fulani.
Ranar Lahadi da rana kuma za a rufe bikin da yin liyafar cin abinci ta ɓangaren gidansu ango a dakin taro na Banquet Hall da ke fadar shugaban ƙasa.
Tsintar dami a kale
Wani bidiyo ya yaɗu a shafukan sada zumunta da ke nuna abokan ango Yusuf a cikin wata motar bas suna gwangwaje direbansu da kyautukan girma.
A motar an ga matasan samarin dukkansu da fararen shaddoji suna tara wa direban kyautar kuɗadɗe, wataƙila don irin zirga-zirgar da ya yi da su daga filin jirgin sama zuwa Bichi, sannan ya kai su birnin Kano.
Matasan sun yi ta wa direban kyautar kuɗi daga mai N50,000 har da masu ba shi dala.
A ƙarshe dai Malam Adamu kamar yadda suke kiran sunansa ya tashi da sama da N500,000 lakadan.
Ƴan Najeriya dai za a iya cewa sun shafe ƙarshen makon nan suna tattauna batun, inda suka kashe ƙwarƙwatar idonsu ta hanyar kalllon hotuna da bidiyon da ake yaɗawa.
Su kuwa al'ummar Bichi, a iya cewa wannan shagali ya zama wata sallar tasu, don ko ba komai sun kashe ƙwarƙwatar idonsu da irin taron da ba a taɓa yi ba a garin.
Su ma dai mutanen birnin Kano, sun bai wa ido abinci, sun kuma yi ta jin rugugin sauka da tashin jiragen sama, wataƙila irin wanda ba su taɓa shaida ba.