Yusuf Buhari da Zahra Bayero: An ɗaura auren ƴar sarkin Bichi da ɗan shugaban Najeriya

An ɗaura auren Yusuf Muhammadu Buhari da Zahra Nasir Bayero a garin Bichi kan sadaki naira 500,000.

Aminu Dantata ne waliyyin amarya yayin da Malam Mamman Daura ne waliyyin ango. Ministan Sadarwa Malam Isa Ali Pantami ne ya daura auren na Yusuf da Zahra.

An ɗaura auren ne da misalin ƙarfe 2:38 na ranar Juma'a.

Manyan jami'an gwamnati da ƴan siyasa da suka haɗa da gwamnoni da ƴan majalisa da ministoci da dai saurensu.

An tsaurara tsaro a gidan Sarkin Bichi da kuma masallacin Bichi, inda a nan ne aka daura auren Yusuf, ɗan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Zahra, ƴar Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero.

Haka kuma akwai jami'an tsaro a duka titunan cikin garin.

Jami'an tsaron fadar shugaban ƙasa ne ke kula da al'amuran tsaro a gidan Sarkin na Bichi da kuma masallacin da aka gudanar da ɗaura auren.

Sannan tun daga cikin birnin Kano har zuwa Bichi an ajiye jami'an tsaro na soja da ƴan sanda a kan tituna.

Sojoji da ƴan sanda da jami'an farin kaya na DSS su ne suka fi yawa sai dai akwai na Civil Defence da kuma Road Safety.

Kusan mafi yawan shaguna da titunan Bichi ba su buɗe ba sai wasi ƴan kaɗan ne suka bude kuma su ma masu sayar da kayan masarufi ne.

Wakilin BBC da ke garin Bichi ya shaida cewa tun da sanyin safiya aka fara share titunan Bichi da na kofar gidan Sarkin.

Ya kuma ce ana iya ganin jama'a musamman jami'an tsaron ƴan sanda sun yi dandazo a wuraren masu shayi domin yin kalaci.

Ana sa rai Shugaba Muhammadu Buhari zai halarci taron ɗaurin auren.

Ɗaruruwan manyan mutane ne, kama daga jam'an gwamnati zuwa sarakuna, za su halarci daurin auren a garin Bichi.

Duka otal-otal na Kano sun yi cikar kwari, har ta kai wasu manyan jami'an gwamnati da wasu shugabannin hukumomin tsaro sun rasa otal din da za su sauka.

Tawagar Shugaban Ƙasa ta isa kano

Tun jiya tawagar gwamnatin tarayya ta isa Kano domin daurin aruren da naɗin sarautar sarkin na Bichi.

Tawagar tana ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ma'aikatan shugaban ƙasa Farfesa Ibrahim Gambari.

Sauran mutanen da ke cikin tawagar sun haɗa da ministan tsaro Bashir Salihi Magashi da na ayyukan noma Sabo Nanono da Sanata Hadi Sirika, ministan jiragen sama da Injiniya Suleiman Hussein Adamu, ministan harkokin ruwa da kuma Mai taimakawa shugaba Buhari kan kafofin yaɗa labarai Malam Garba Shehu, kamar yadda wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Malam Garba Shehun ta bayyana.

Haka kuma, sanarwar ta ce Malam garba Shehu zai zauna a Kano bayan ɗaurin auren inda zai wakilci Shugaba Buhari a wurin naɗin sarautar Sarkin Bichi wanda za a yi ranar Asabar.