Abin da ya sa wasu jihohi ke kwashe ɗalibansu daga Jami'ar Jos

Jami'ar Jos

Asalin hoton, Other

Ɗalibai da ke karatu a Jami'ar Jos da ke jihar Filato a tsakiyar Najeriya sun shiga wani yanayi na fargaba sakamakon matsalolin tsaro bayan wani rikici da ya yi ajalin wasu daga cikinsu.

Wannan yanayi ya kai ga hukumar makarantar bayar da umarni dakatar da karatu tun bayan samun hatsaniyar a karshen mako.

Yanayin da ake ciki yanzu haka a garin Jos ya soma tilasta wa wasu gwamnatoci kokarin ganin yadda za su kwashe ɗalibansu da ke karatu a Jami'ar.

Wasu rahotanni na cewa da dama daga cikin ɗaliban sun shiga tsaka-mai-wuya da yanayi na fargabar tsaro.

Wani ɗalibin jami'ar ya shaida wa BBC cewa jihohi da dama ne suka tura motoci suka kwashe ɗalibansu.

Ya ce jihohin sun haɗa da Benue da Nasarawa da Gombe da wasu na kudancin ƙasar. Tun lokacin da aka samu rikici ne kuma ɗaliban ƴan asalin jihar Filato suka fice daga jami'ar, a cewar ɗalibin.

Akwai kuma gwamnatin Kebbi da ta tura da tallafin kudi ga ɗalibai ƴan asalin jiharta.

Wane hali ɗaliban ke ciki?

Ɗaya daga cikin ɗaliban jami'ar ya ce da dama daga cikin ɗaliban sun shiga ruɗani ne saboda tsoron rayuwarsu.

Saminu Inuwa da ke aji hudu a tsangayar fanin nazarin ilimin addinin Musulunci ya ce tun ranar 18 ga watan Agusta suke cikin ɗimauta abin da ya kai ga wasu ɗaliban na guduwa daga garin Jos.

Ya ce duk da cewa yanzu kura ta lafa kuma hukumomin makaranta na ƙoƙarin wajen ba su tsaro, da dama hankalinsu ya koma gida.

Sannan ya ce a yanzu ba a san lokacin komawa karatu ba, amma hukumar makaranta ta umarci duk wani ɗalibi da ke cikin makaranta kada ya fita ya zauna a ɗakunansu na kwana.

Saminu ya kuma ce: "Ana ta kawo musu ɗauki, wasu ɗaliban ma ana turowa a kwashe su, amma a halin yanzu lamarin tsaronsu ya inganta"

Yawanda ɗaliban da jihohi suka kwashe

Wata kungiya ta dalibai mazauna birnin tarayya Abuja ta ce ta kwaso dalibai 279 daga Jami'ar.

Sanann gwamnatin Ogun na cewa ɗalibanta 80 da suka maƙale a wannan yanayi an kwaso su. Abia ta bada rahotan kwashe ƴan jihar sama da 200 da ke karatu a Jami'ar.

Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu ya ware naira miliyan biyar domin tallafa wa ɗalibai 'yan asalin jihar 95 da ke karatu a Jami'ar.

Hukumomin ilimi na jihar Kebbi sun ce sun ɗauki matakin ne domin tallafawa ɗaliban a lokacin da ɗaliban ke buƙatar taimako.

Short presentational grey line

Jihohi na daukan waɗanan matakai ne duk da cewa gwamnan Filaton, Simon Lalong ya roƙi gaffara kan kashe mutum 23 wadanda fada ta ritsa da su.

A ranar 14 ga watan Agusta ne wasu matasa da ake zargin 'yan ƙabilar Irigwe ne suka tare wa wasu matafiya Musulmai hanya suka kashe 27 daga ciki sannan suka raunata wasu da yawa yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Jihar Ondo daga Bauchi.

Saboda gudun abin da ka iya biyo baya, gwamnatin Filato ta saka dokar hana fita a kananan hukumomi uku na Jos tsawon awa 24, kodayake an sassauta daga baya.

Sai dai duk da wannan doka an ci gaba da samun rikici da kashe-kashe abin da ya kai ga an hallaka wasu ɗaliban jami'ar Jos.

Wannan yanayi ya tilastwa hukumomin jami'ar dakatar da karatu sannan ta umarci kowanne dalibi ya zauna a cikin makaranta banda fita.

Kana majiyoyinsu sun tabbatar da cewa an kewaye makaranta da jami'an tsaro.