Shugabar Tanzania Samia: Mun hau mulki ne domin nuna cewa mata za su iya jagoranci

President Samia Suluhu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Samia Suluhu Hassan ta sha rantsunwar kama aiki wata biyar da suka wuce
    • Marubuci, Daga Salim Kikeke
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa, Dar es Salaam

Shugabar Tanzania ta ce akwai mutanen da suka nuna shakku kan dacewarta wajen shugabancin kasar lokacin da ta zama shugabar kasa saboda ita mace ce.

Wasu "ba su yarda cewa mata za su fi maza iya shugabancin kasa ba don haka mun zo nan ne domin mu nuna musu cewa mata za su fi maza iya jagoranci," a cewar Samia Suluhu Hassana hirarta da BBC.

A watan Maris aka rantsar da matar mai shekara 61 a matsayin shugabar kasar Tanzania bayan mutuwar Shugaba John Magufuli.

Yanzu haka ita ce mace kadai da ke shugabancin kasar Afirka a siyasance. Shugabar kasar Ethiopia ta je-ka-na-yi-ka ce.

"Da farko wasu daga cikin ma'aikatan gwamnatina sun nuna shakku akaina suna ganin kamar kowacce mace ce, amma daga bisani suka amince da jagorancina," in ji Ms Samia.

Ta kara da cewa "Amma hakan ba wai kawai yana faruwa ba ne a Afirka, ko da a Amurka [Hillary] Clinton ta kai matakin da muka yi tsammanin za ta zama shugabar kasa amma hakan ya gagara."

Ms Samia ta ce mayar da hankali kan tsare-tsaren ci gaban kasa da kuma ayyukan da jama'a suke so su ne hanya kadai da za ta kawar da adawar da ake yi mata.

Ta kara da cewa duk da kalubalen da kasashe irin su Liberia da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka suke fuskanta, wasu kasashen za su iya koyi da su saboda shugabanni mata da suke da su.

Shugaba Samia ta maye gurbin John Magufuli wanda ya rasu sakamakon bugun zuciya, kamar yadda ta bayyana a wancan lokacin.

An zargi Magufuli da musguna wa 'yan hamayya da hana fadin albarkacin baki. Sai dai ana kallonta a matsayin wadda za ta kawo sauyi a shugabancin kasar.

Amma kamun da aka yi wa shugaban 'yan hammayar kasar Freeman Mbowe kwanakin baya kan zarge-zargen da ke da alaka da ta'addanci ya sa wasu na ganin Shugaba Samia na neman ci gaba da tsari irin na magabancinta.

Freeman Mbowe

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Freeman Mbowe ya sha sukar marigayi shugaban Tanzania John Magufuli

Sai dai shugabar ta Tanzania ta kare matakin tana mai cewa zarge-zargen da ake yi wa Mr Mbowe "ba na siyasa ba ne" domin kuwa tun watan Satumbar shekarar da ta wuce ake gudanar da bincike a kansa.

"Ya kwashe tsawon lokaci ba ya kasar. Ban san dalilin da ya sa ya gudu ba amma lokacin da ya dawo sai ya soma haifar da rashin kwanciyar hankali inda ya rika kiraye-kiraye a samar da sabon tsarin mulki

"Ina tsammani ya yi amfani da wannan dama ce domin idan aka kama shi zai ce an yi hakan ne saboda ya yi kira a samar da sabon kundin tsarin mulki maimakon ainihin zarge-zargen da ake yi masa," in ji shugabar.

An tsare Mr Mbowe bayan ya ce zaben da ya gabata yana cike da magudi.

Shugaba Samia ta ce za ta "bari kotuna su yanke hukunci kan ko yana da laifi ko kuma ba shi da shi".

Kazalika shugabar Tanzania ta ce a shirye take ta gana da shugabannin 'yan hamayya da ma sauran masu ruwa da tsaki domin su tattauna kan sauya kundin tsarin mulki "idan lokaci ya yi" sai dai ba ta fadi lokacin da za ta yi hakan ba.

Masu suka na zargin cewa kundin tsarin mulkin kasar ya nuna fifiko ga jam'iyya mai-ci ta Chama Cha Mapinduzi.

Samia Suluhu Hassan

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugaba Samia ta sauya kallon da 'yan Tanzania suke yi wa cutar korona

Shugabar ta dauki wani salo game da yaki da cutar korona wanda ya sha bamban da na Magufuli, mutumin da ya rika nuna shakku kan cutar.

Ms Samia ta ce yanzu haka tana kamfe na ganin an kara yawan riga-kafin cutar. Ta ce ya yanke shawarar yin allurar riga-kafin korona a bainar jama'a ne domin nuna cewa ba ta da wata illa.

"Amma babbar damuwata yanzu ba dari-darin da ake yi kan riga-kafin ba sai dai samun riga-kafin, mun karbi gudunmawar riga-kafin daga Amurka sanna mun sayi wasu daga Covax, amma sun kusa karewa," a cewar Ms Samia.

Woman sing a phone

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, 'Yan kasar Tanzania suna amfani da shafukan sada zumunta wajen sukar gwamnati

Kazalika Samia ta kare matakin gwamnatinta na tilasta dokar da ta takaita 'yancin 'yan jarida.

Ta ce 'yan jarida "suna da damar yin aiki idan dai suka yi biyayya ga dokokin kasar".