Hisbah: Hukumar ta ce yaɗa hotunan Zarah Nasir Bayero haramun ne

Zarah Nasir Ado Bayero

Asalin hoton, Other

Bayanan hoto, Ana sa ran za a yi bikin Zarah Nasir Ado Bayero da Yusuf Buhari a watan Agusta

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da ke arewacin Najeria ta yi kira ga masu yaɗa hotunan 'yar Sarkin Bichi, Zarah Nasiru Ado Bayero wadda ɗan shugaban ƙasa Yusuf Buhari zai aura, da su guji yin hakan "saboda ya saɓa wa Shari'ar Musulunci".

Kwamandan Hisbah Harun Muhammad Ibn-Sina ya ce aikin hukumar shi ne hana yaɗa ɓarna ko da kuwa ta faru a baya, ba wai "tonowa da kuma hukunta mutum ba".

Kiran na Hisbah ya biyo bayan dubban ra'ayoyi da mutane suka dinga bayyanawa a shafukan zumunta cikin kwana uku da suka wuce bayan hotunan amarya Zarah sun karaɗe shafukan sanye da wata doguwar riga.

A cikin hotunan waɗanda ba a gan ta tare da angon ba, babu ɗan kwali a kan gimbiyar ta Masarautar Bichi da ke Kano sannan kuma saman rigar yana da launin fatar jikinta.

Wasu bayanai sun ce hotunan sun ɓulla ne daga wani bikin mata zalla da aka gudanar a Abuja a wannan makon.

Wannan ne ya sa masu amfani da shafukan zumunta suka dinga kira ga Hisbah da ta ɗauki mataki, inda sunan hukumar ya kasance ɗaya daga cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a kafofin na Najeriya tun daga ranar Laraba zuwa Juma'a.

'Haramun kuke aikatawa'

Zarah Nasir Ado Bayero

Asalin hoton, Other

Bayanan hoto, A hotunan da aka yaɗa na Zarah Nasir Bayero, ba a gan ta tare da ango Yusuf Buhari ba

Hukumar Hisbah ta Kano wadda aka sani da tabbatar da bin dokokin Musulunci, ta ce yaɗa hotunan "ya saɓa wa Shari'ar Musulunci".

Cikin wata hira da manema labarai, Kwamandan Hisbah Harun Muhammad Ibn-Sina ya ce ba aikin hukumar ba ne tonowa tare da kama masu laifi, aikinsu shi ne hana yaɗa ɓarna.

"Shakka babu yadda ake yaɗa hotunan auren nan ya saɓa wa ƙa'ida ta Shari'ar addinin Musulunci. Ta iya yiwuwa wannan al'amari a fili aka yi shi ko kuma a ɓoye...amma kai da kake yaɗawa kana nuna wa waɗanda ba su san an yi ba.

"Waɗanda suka fito da wannan hoto idan da gangan suka yi su ji tsoron Allah kar su sake yaɗa shi.

"Idan ma wa'azi za ka yi sai dai ka ce abin da aka yi na kaza ba daidai ba ne kuma ina bayar da shawara - amma ba wai ka yaɗa hoton ba ta yadda za a gan ta a cikin wani hali."

'Idon duniya yana kansu a matsayinsu na 'ya'yan manya'

Kwamanda Ibn-Sina ya ce kasancewar Zarah 'yar sarki da kuma Yusuf ɗan shugaban ƙasa, duniya za ta saka musu ido saboda "su ababen koyi ne".

"Duk wata shiga wadda wani zai yi a yi shuru, to su idan suka yi ɗaukarta za a yi a nuna wa duniya; wani don a tozarta su; wani da niyyar a ƙasƙanta Musulunci," a cewarsa.

Presentational grey line

Duk da wasu na sukar hotunan da ke yawo a shafukan sada zumunta musamman saboda gidan da ta fito, wasu kuma na ganin hotunan ba su yi munin da har za a dinga ce-ce-ku-ce ba a bikin da aka yi na mata zalla.

Irin wannan saɓanin ba wani sabon abu ba ne a arewacin Najeriya inda addinin Islama da al'ada suka fi yin tasiri sosai.

Presentational grey line

Wasu labaran da za ku karanta:

Bayanan bidiyo, Bidiyon shirin Zamantakewa: Shawarwari ga namiji mai mace fiye da ɗaya
Presentational grey line