Ana tuhumar Amarya da hannu a kisan angonta

Ango ya mutu ne kwanaki bayan aurensa
Bayanan hoto, Gemechis Mosisa

An kama mutane shida a kasar Habasha dangane da mutuwar wani ango ciki har da matarsa.

An tsinci gawar Gemechis Mosisa kwanaki bayan aurensa a garin Nekemte da ke yammacin Habasha.

Ma'aikacin jinyar, mai shekara 28, ya wallafa wani sakon daurin aure a shafin Facebook a ranar Asabar kuma washe gari ya saka hotunan bikin.

''A cikin cocin aka daura wa Gemechis aure kuma bikin auren gwanin ban sha'awa,'' in ji yar uwarsa Chala Inkosa.

" Iyalinsa na cikin bakin ciki bayan da murnarsu ta koma abin takaici''.

Iyalinsa sun ce a ranar Lahadin da ta gabata ne aka yi masa gani na karshe bayan ya bar gida, an yi tsammani daga baya zai halarci liyafar da aka shirya masa a gidan surukansa amma bai je ba.

Lokacin da 'yan uwa da abokansa suka sanar da bacewarsa , 'yan sanda sun fara nemansa kuma bayan kwana biyu suka gano gawarsa a cikin wani karamin tafki da ke wajen gari.

An gano kwat dinsa rataye akan bishiyar da ke kusa.

An kuma gano zobensa na zinari da agogonsa a cewar shugaban masu bincike a garin Nekemte Misganu Wakgari, ya kuma kara da cewa ana ci gaba da bincike.

A ranar Alhamis ne aka binne gawar angon inda mutane da dama a shafukan sada zumunta suka bayyana alhini a kan al'amarin.