Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Kane, Haaland, Lukaku, Trippier, Messi, Ramsey, Asensio, Ward-Prowse

Tayin da Manchester City ta yi na sayen kyaftin din Ingila Harry Kane ya kasa da fam miliyan 40, a farashin da Tottenham ta sanya wa dan gaban mai shekara 27 na fam miliyan 160. (Jaridar Star)

Har yanzu Chelsea ba ta karaya ba a kan burinta na sake sayo tsohon dan wasanta na Belgium, da ke Inter Milan, Romelu Lukaku mai shekara 28. (Jaridar Athletic)

A cikin 'yan kwanakin da ke tafe ne a hukumance Barcelona za ta bayyana sabon kwantiragin shekara biyar da ta kulla da dan gabanta na Argentina Lionel Messi mai shekara 34. (Jaridar Sport)

Newcastle United ta tuntubi Juventus a kan yuwuwar sayen dan wasan tsakiya na kungiyar ta Italiya, dan Wales Aaron Ramsey, mai shekara 30. (Jaridar Goal)

Manchester United tana da tsawon wata 12 ta shawo kan dan gaban Borussia Dortmund, Erling Braut Haaland cewa ita ce kungiyar da ta fi dacewa da shi.

A bazarar shekara mai zuwa ne ake sa ran dan wasan na Norway mai shekara 21, wanda Chelsea da wasu kungiyoyi da dama ke so, zai koma wata kungiyar, a lokacin da yarjejeniyarsa ta Dortmund ta bayar da damar biyan fam miliyan 75, kudin na-gani-ina-so, bayan farashinsa. (Jaridar Manchester Evening News)

Aston Villa ta kara tayi na biyu a kan dan wasan tsakiya na Southampton, James Ward-Prowse, dan Ingila, bayan an ki tayinta na farko na fam miliyan 25. (Jaridar Mail)

Leicester City da Leeds United da kuma Everton na gogayya domin sayen dan wasan gaba na gefe na Real Madrid Marco Asensio, dan Sifaniya mai shekara 25. (Jaridar Fichajes)

Atletico Madrid na shirya wa tafiyar dan bayanta Kieran Trippier mai shekara 30, wanda ake sa ran zai koma Manchester United, inda take shirin sayen Alessandro Florenzi, na Roma mai shekara 30 domin maye gurbin dan tawagar ta Ingila. (AS - in Spanish)

Sheffield United na tattaunawa domin sayen tsohon dan wasan tsakiya na tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21 Ronaldo Vieira, mai shekara 23, daga Sampdoria. (Jaridar Mail)

Newcastle United na shirin sayen dan wasan tsakiya Boubacar Kamara mai shekara 21, dan Faransa daga Marseille a kan kusan fam miliyan 10. (Jaridar Mail)

Kociyan Roma Jose Mourinho na sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund Thomas Delaney dan Denmark mai shekara 29, bayan da kungiyar ta kasa samun Granit Xhaka na Arsenal, dan Switzerland, mai shekara 28. (Jaridar Sun)

Tottenham ta fara tattaunawar sharar fage da Wolves a kan sayen Conor Coady, inda kociyan Spurs din Nuno Espirito Santo ke sha'awar sake hadewa da dan bayan dan Ingila mai shekara 28, a arewacin London. (Football Insider)

Kociyan Inter Milan Simone Inzaghi ya kuduri aniyar ci gaba da kokarin dauko dan bayan Chelsea, Marcos Alonso, dan Sifaniya mai shekara 30. (Jaridar Calciomercato)

Wasu rahotanni na cewa Arsenal da Everton na son sayen dan wasan gaba na Schalke, Matthew Hoppe, dan Amurka mai shekara 20. (Jaridar Star)

Ana danganta Willy Caballero da komawa kungiyar Malaga ta Sifaniya, bayan da Chelsea ta saki golan dan Argentina a bazaran nan (Jaridar Marca)

Norwich City ta fara tattaunawa da Bournemouth kan sayen dan wasan tsakiya Philip Billing, dan Denmark mai shekara 25. (Jaridar Football Insider)