Abubakar Malami: Ministan Shari'a ya musanta cewa Atiku Abubakar ba ɗan Najeriya ba ne

Lokacin karatu: Minti 3

Ministan Shari'a na Najeriya ya musanta wasu rahotanni da kafafen watsa labarai suka bayar cewa ya fada wa wata kotu cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar bai cancanci tsayawa takarar shugabancin ƙasar ba, don ba haifaffen Najeriya ba ne.

Abubakar Malami ya ce shari'ar da ake magana a kai wata ƙungiya ce mai suna "Incorporated Trustees of Egalitarian Mission for Africa" (EMA) ce ta shigar da ita tun a shekara ta 2019 kuma shi ma yana cikin wadanda ake ƙara.

Ministan ya yi martanin ne bayan ce-ce-ku-cen da ake ta yi sakamakon labarin da wasu jaridun Najeriya suka wallafa cewa Abubakar Malami ya ce Atiku Abubakar bai cancanci takarar shugabanci Najeriya ba saboda lokacin da aka haife shi garinsu na ƙarƙashin Jamhuriyar Kamaru.

Ɗaya daga cikin jaridun Najeriya Pulse ta rawaito cewa ministan na cewa an haife Atiku a garin Jada na Adamawa a 1946 a lokacin garin yana karkashin ikon kasar Kamaru - sai bayan shekara ta 1961 garin ya koma karkashin Najeriya.

Jaridar ta ambato ministan yana cewa bisa wannan dalili tsayawar Atiku takara ta saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Wannan batu ya ja hankali sosai a faɗin ƙasar musamman a kafofin sada zumunta inda mutane suka rinƙa bayyana mabambanta ra'ayi.

FS Yusuf @FS_Yusuf_ Sun soma ganin Atiku a matsayin babbar barazana a 2023 shiyasa irin wadannan kamalai ke fitowa daga bakin Malami. Kotun ƙoli ta wanke Atiku, amma Malami ya san hanyar ruguza ɗan siyasa a Arewa ta hanyar zubar da mutuncinsa. Duk mai gaskiya na cikin bala'i.

Malachy Odo II @MalachyOdo1; Batun muhawarar da ake tafkawa a gaban kotun tarayya kan Antoni Janar Malami kan batun Atiku ba ɗan ƙasa bane don haka ba zai iya takara ba a wannan ƙasa bai cancanci takardar da aka yi rubutun ba, bata lokaci kotu ne.

Me Malamin ke cewa?

A zantawarsa da BBC, Abubakar Malami ya ce wata ƙungiya ce ta shigar da wannan ƙara tun gabannin zaɓen 2019, lokacin da ake taƙaddama kan cancantar ɗan takara.

Ya ce shi kansa an kai shi ƙara domin ya amsa tambayoyi ko yi wa kotu bayani kan Atiku Abubakar, don haka babu gaskiya a ce shi ya shigar da ƙara

"Wannan ƙara ce da aka shigar tun kafin zaɓen 2019, tana cikin jeren ƙararrakin da aka shigar a baya kamar irin na Shugaba Buhari kan batun takardun ba shi haƙƙin tsayawa takara," in ji Malami.

Ministan ya ce bai yi mamakin sake bijiro da wannan batu ba a yanzu domin a makon da ya gabata Jaridun Premium Times da Sahara Reporter sun yi ƙoƙarin shigo da ɓatanci a kan ofishin Antoni Janar da shi kansa Malami.

Ya ce "Jaridun na ƙoƙarin nuna cewa an yi amfani da ni da shugaban ma'aikatan fadar gwamnati da ministan kuɗi cewa mun yi ƙoƙarin tursasa wa gwamnan babban bankin Najeriya ya biya wasu kuɗaɗe da suka kai biliyan sama da 500 wanda kuma babu gaskiya a ciki".

Sannan ya kuma shaida cewa duk ana kitsa irin wadannan batutuwan ne domin zubar da mutuncin Antoni Janar da kuma shiga tsakaninsa da sauran abokan hulda ta fuskar tarayya.

Ya ce shiri da aka kitsa da zummar zubar da mutuncinsa a fuskar ƴan Najeriya shi ya sa ake danganta sunansa da abubuwa daban-daban saboda duk wanda ya san tsarin mulki irin na Najeriya zai fahimci yana da iyaka.

Karin haske

An sha dai dora alhakin abubuwa da dama da ke faruwa a Najeriya kan Antoni Janar, Abubakar Malami.

Ko a lokacin sauya shugaban EFCC Ibrahim Magu an zargi hannun Malamin, hakazalika lokacin marigayi Abba Kyari da tsige Sarki Muhammadu Sunusi na biyu, kuma wasu abubuwa da dama da ke faruwa da taƙaddama da ake yawaita samu a gwamnatin tarayya.

Sai dai kamar yadda Malamin ya shaida wa BBC, babu gaskiya a irin waɗannan zarge-zarge.