Abin da ya sa ba mu ɗauki mataki ba kan auren ɗan Malami - Gwamnatin Kano

Gwamnatin Kano ta shaida wa BBC cewa babu wanda ya kai korafin cewa mutane sun karya ka'idojin da aka gindaya don kaucewa kamuwa da korona a bikin dan ministan shari'a Abubakar Malami wanda aka gudanar a makon da ya gabata, shi ya sa ba su dauki mataki ba.

Hotunan bidiyo da aka rinka wallafawa a shafukan sada zumunta, sun nuna yadda mutane cunkus ke ta rakashewa suna liki da kudi a bikin Abdulazeez Malami da Khadija Dambata, wanda hakan ya saba sharuddan da gwamnatin tarayya da ta jihar ta gindaya wa mutane don dakile yaduwar annobar korona.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Muhammad Garba ya ce, bangaren shagalin bikin da gwamnatin Kano ta shirya a fadarta an bi umarnin bai wa juna tazara sosai.

''Kuma ce-ce-ku-ce da ake kan wannan biki da aka gudanar, ba mu samu rahoto ko guda da ke tabbatar da cewa mutane sun karya ka'idojin korona a wurin bikin ba, don haka ba mu da hujjar daukan mataki.''

''Kazalika batun bikin da muka dau nauyi a fadar gwamnatin Kano mun bi duk matakan kariya daga korona sai dai ba mu san abin da ya faru a wani wajen ba cikin shagulgulan bikin, hasalima babu wanda ke da hujjar cewa akwai wasu mutane da suka karya dokoki a bikin da aka gudanar a Kano.'' Kalaman Muhammad Garba kenan.

Sai dai sabanin wadannan kalamai na kwamishinan, hoton da aka dauka a gidan gwamnatin Kano ya nuna yadda gwamnoni da sauran mutane suka cakudu wuri guda a hoto babu wata tazara tsakaninsu.

Wanene Abubakar Malami?

Mutane da dama na yi wa Malami ganin daya daga cikin makusanta ko na hannu daman Shugaba Muhammadu Buhari.

Yadda mutane suka cika bikin dansa, Abdulazeez Malami a ranar Asabar, ya nuna cewa yana da tasiri sosai tsakanin masu rike da mulki, wannan dalilin ne ya sa mutane ke diga ayar tambayar sanin wanene Malami?

An haife ministan shari'ar a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya a shekara ta 1967, kuma a can ya kammala firamare da sakandare kafin ya je jami'a a Sokoto inda ya karanci fanin shari'a.

A shekara ta 1992 aka tabbatar da shi a matsayin lauya, sannan a 1994 ya je jami'ar Maiduguri inda ya yi digiri na biyu a fanin sha'anin shugabanci.

Masu sharhi kan harkokin siyasa sun ce alakar Malami da Shugaba Buhari ya soma ne lokacin da ya zama lauyan tsohuwar jam'iyyar Buhari ta CPC a 2010.

Daga nan, Malami da Buhari tafiyarsu ta ci gaba da kasancewa tare a fannin siyasa da kuma lokacin da ya takawa jami'yyar APC rawa ta musamman a 2014.

Bayan rashin nasararsa a lokacin da Malami ya nemi kujerar gwamna a 2014, Shugaba Buhari ya nada shi minista mafi karancin shekaru a 2015 - a matsayin ministan shari'a, kuma har yanzu yana kan wannan mukamin.

Karin labaran da zaku so karantawa