Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ba ni da hannu a cire Sanusi II – Abubakar Malami
Ministan shari'ar Najeriya kuma babban Antony Janar nan kasar Abubakar Malami ya wanke kansa inda ya ce ba shi da hannu a tsige Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
A wata sanarwa da maitaimaka masa kan yada labarai Dakta Umar Jibril Gwandu ya fitar, ya bayyana cewa ministan shari'ar bai da hannu a cire sarkin da kuma tsare shi a jihar Nasarawa da aka yi.
Ya ce an mika batun wadanda suka taka rawa a badakalar cire sarkin gaban sharia domin yanke hukunci. Batu ne da yake gaban kotu
Ya bayyana cewa ministan shari'ar a halin yanzu ba zai ce komai ba kan batun da ke gaban sharia'a.
A makon da ya gabata ne dai aka tsige Muhammadu Sanusi II daga kan kujerarsa ta sarkin Kano inda aka tura shi garin Loko, daga bisani kuma zuwa garin Awe.
Bayan 'yan kwanaki kuma bayan lauyoyin tsohon sarkin sun kai kotu, aka bai wa sarkin 'yancin walwala inda ya tafi Legas.
Ko bayan tsige sarkin, itama Fadar Shugaban Najeriya sai da ta fito ta wanke kanta kan zarginta da ake yi da hannu a cire sarkin inda mai magana da yawun shugaban kasar ya bayyana cewa shugaban kasar bai da hannu a tsige Muhamadu Sanusi II