Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Coronavirus ta bulla a kasashen Afirka 26

Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen duniya har da rahotanni kan coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Karshen rahotannin ke nan

    Jama'a mu kwana lafiya.

    Ku duba kasa domin karanta labaran da kuma komawa babban shafin namu domin kallon hotuna da bidiyo har da ma wasu labaran.

  2. Buhari ya jajanta wa jama'ar Lagos

    Shugaba Muhammadu Buhari ya jajanta wa iyalan wadanda hatsain fashewar gas ta rutsa da su a Karamar Hukumar Amuwo Odofin ta jihar Legas, wadda ta faru ranar Lahadi.

    Shugaban ya mika ta'aziyyarsa ga gwamnatin Jihar Legas da kuma mazauna jihar baki daya.

    Mutane da dama ne suka ji rauni bayan an samu fashewar gas da tsakar ranar Lahadi.

    A wata sanarwa da mai taimaka wa Buhari kan kafafen yada labarai Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce bai "ji dadin labarin ba".

    "Yayin da kamfanin NNPC yake kokarin gano musabbabin fashewar, ina mika ta'aziyyata ga wadanda abin ya shafa da iyalansu da gwamnatin Legas da kuma jama'ar jihar," in ji Buhari.

  3. Coronavirus: Mutum 800 sun kamu a rana guda a Switzerland

    Da tsakar kowace rana, gwamnatin kasar Switzerland ke fitar da sabbin bayanai game da cutar coronavirus.

    Jama'ar kasar sun sha mamaki a yau Lahadi, inda suka ga mutum 800 sun kamu a cikin sa'a 24 kacal - abin da ya sa yawansu ya kai 2,200 gaba daya.

    Kusan komai ya sauya a kasar. Iyaye na neman gidajen rainon yara bayan sanarwar ranar Juma'a da ta ce za a rufe makarantu daga gobe Litinin.

    Dubban mutanen da suka sayi tikitin tafiya hutun Easter zuwa kasashen waje wajibi ne su soke tafiyar: kasashe 'yan kadan ne a yanzu 'yan Switzerland za su iya shiga.

  4. APC ta lashe zaben cike gurbi a Jigawa

    A wani labarin kuma - wanda ba na coronavirus ba - jam'iyyar APC ta lashe zaben cike gurbi a Mazabar Dan Majalisar Tarayya ta Babura/Garki, wanda aka gudanar a yau Lahadi.

  5. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus: Mutum 368 sun mutu a Italiya a rana guda

    Mutum 368 ne suka mutu a rana guda a kasar Italiya, wani sabon tarihi maras kyau na rana guda.

    Yankin da cutar ta fi kamari a kasar mai suna Lombardy, shi ne yake da 252 daga cikin mamatan.

    A kasar baki daya, mutanen da suka mutu sun haura 1,800.

  6. Labarai da dumi-dumi, Afirka ta Kudu ta kafa dokar-ta-baci, za ta rufe makarantu

    Afirka ta Kudu za ta rufe makarantu sakamakon yaduwar cutar coronavirus na tsawon kwana 30 kuma matakin zai fara aiki daga ranar Laraba.

    Shugaban kasar Cyril Ramaphosa ne ya bayyana hakan a wani jawabi da yake gudanarwa yanzu haka ga 'yan kasar.

    Shugaban ya bayyana cewa an dakatar da kai ziyara gidajen yari a kasar.

    Kazalika jami'an gwamnatin kasar za su rika ganawa sau uku a mako domin sa ido kan yaki da cutar.

  7. Labarai da dumi-dumi, Mutum na 4 ya kamu da coronavirus a Kamaru

    An samiu mutum na hudu da ya kamu da cutar coronavirus a kasar Kamaru.

    Ministan lafiyar kasar ne ya tabbatar da hakan.

  8. Coronavirus ta bulla a kasashen Afirka 26

    A cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters, Zuwa yanzu, Lahadi 15 ga watan Maris, cutar coronavirus ta bulla kasashen Afrika 26. Su ne:

    Morocco, Tunisia, Egypt, Algeria, Senegal, Togo, Cameroon, Burkina Faso, Democratic Republic of Congo, South Africa, Nigeria, Ivory Coast, Gabon, Ghana, Guinea, Sudan, Kenya, Ethiopia, Mauritania, Rwanda, Seychelles, eSwatini, Namibia, Central African Republic, Congo Brazzaville and Equatorial Guinea.

  9. Kure karya

    Ministan Lafiyar Afirka ta Kudu, Dr Zweli Mkhize ya karyata rahotannin da ke cewa kasarsa za ta rufe makarantu domin dakile yaduwar cutar coronavirus.

    Ministan ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa "labarin kanzon kurege" ne.

  10. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus: Mutum 14 sun mutu a Birtaniya

    Wasu mutum 14 sun mutu sakamakon cutar coronavirus a Birtaniya, abin da ya kai adadin zuwa 35, in ji hukumar lafiyar kasar.

    Hukumar ta kara da cewa mutum 1,372 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a Birtaniya ya zuwa ranar Lahadi, sun karu daga 1,140 a ranar Asabar.

  11. Jami'ar Ghana ta dakatar da karatu saboda Coronavirus

    Hukumomin jami'ar University of Ghana sun dakatar da karatu bayan samun rahoton kamuwa da cutar Covid-19 da wani dalibin jami'ar ya yi.

    Jaridar Citi NewsRoom ta Ghana da ake wallafawa a intanet ta rawaito cewa, jami'ar ta kuma hana daliban da ba 'yan kasa ba shiga harabar jami'ar har sai sun ji daga gare ta.

    Mataimakin shugaban jami'ar ya tabbatar wa da 'yan jami'ar irin kokarin da mahukunta ke yi na ganin bayan cutar a jami'ar.

    Sai dai rahotannin sun ce ba a rufe jami'ar ba har sai an kammala bin diddigin wadanda ake tunanin mai dauke da cutar ya yi mu'amala da su.

  12. Coronavirus: Hukumomi a Najeriya na sa ido kan maras lafiya a Enugu

    Hukumar kiyaye yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC ta ce tana sane da wani maras lafiya a Jihar Enugu da ake zargin yana dauke da kwayar cutar coronavirus.

    Hukumar ta ce wannan yana daya daga cikin rahotanni da dama da take karba a cibiyar aikin gaggawa ta Emergency Operations Centre.

    "Maras lafiyar yana killace yanzu haka kuma an dauki jininsa, yayin da ake jiran sakamako zuwa gobe (Litinin)," NCDC ta bayyana a shafinta na Twitter.

    A wani rahoton da ta fitar na daban a ranar Lahadi, NCDC ta tabbatar da cewa mutum biyu da suka kamu da cutar a Najeriya sun warke. Ta kara da cewa har yanzu ba a kuma samun mutumin da ya kamu ba.

    Sai dai sakamakon gwajin da aka yi wa maras lafiyar na Enugu ne zai tabbatar ko cutar na nan ko kuma a'a.

  13. Ghana za ta hana baki shiga kasar saboda coronavirus

    Ghana za ta hana baki shiga kasar - wadanda suka taba shiga wata kasa da take da akalla mutum 200 masu cutar coronavirus a cikin mako biyu da suka gabata - kuma zai fara aiki ne daga ranar Talata.

    Ma'aikatar yada labaran kasar ce ta bayara da wannan sanarwa, inda ta umarci kamfanonin jiragen sama da kada su dauki irin wadannan mutanen.

    'Yan kasar Ghana da kuma wadanda ke da izinin zama a kaar ne kadai hanin ba zai shafa ba.

    Kazalika sanarwar ta ce wadanda suka samu damar shiga kasar wajibi ne su killace kansu na tsawon mako biyu.

    Kazalika duk matafiyin da ya nuna alamun cutar ta Covid-19 za a gwada nan take sannan a killace shi.

  14. Kenya za ta kulle kasarta da rufe makarantu

    Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bayar da sanarwa cewa Kenya za ta haramta wa duk matafiyan da suka fito daga kasashen da suke da coronavirus shiga kasar.

    'Yan kasar ta Kenya ne kadai hanin ba zai shafa ba da kuma wadanda ke da izinin zama a kasar - su ma sai in sun yarda za a killace su.

    Mista Kenyatta ya ce haramcin zai fara aiki ne cikin sa'o'i 48 sannan kuma na tsawon kwana 30. Idan akwai bukata, hukumar agajin gaggawa ta National Emergency Response Committee za ta iya kara yawan kwanakin.

    Bugu da kari, daga ranar Litinin za a kulle makarantu baki daya a kasar. Su kuma jami'o'i za su rufe ne daga ranar Juma'a.

    Kenya ta tabbatar da bullar cutar a ranar Juma'a. Shugaban ya ce tun daga lokacin ne kuma karin wasu mutum biyu suka kamu.

  15. Gobarar Legas ta tilasta wa daruruwan mutane hijira

    Daruruwan mutane ne ke gudun hijira daga Unguwar Festac da Abule Ado a Legas sakamakon gobarar da ke ci gaba da ci a halin yanzu.

    Tun a safiyar yau Lahadi jami'an kwana-kwana da sauran jami'an bada agaji ke kokarin kashe wutar amma abin ya ci tura.

    Tuni hukumar kare lafiya ta jihar Legas ta fitar da wata sanarwa inda ta bukaci mazauna yankin da lamarin ya faru su bayar da tazara har sai an gano bakin zaran.

  16. Jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga a Nijar

    Jami’an tsaro a Jamhuriyar Nijar sun yi yunkurin hana jama’a gudanar da zanga-zanga a fadin kasar a ranar Lahadi.

    Dama kungiyoyin farar hula ne suka kira a gudanar da gangamin a fadin kasar domin kara matsa wa gwamnati lamba ta dauki mataki game da jami’an da aka zarga da hannu a badakalar cin hanci da rashawa a ma’aikatar tsaron kasar.

    Wani kwamitin gwamnati ne ya gudanar da bincike kan yadda aka kashe makudan kudade a ma’aikatar tsaron a daidai lokacin da kasar ke fama tabarbarewar tsaro musamman ayyukan masu tayar da kayar baya kamar Boko Haram da kuma kungiyoyi masu alaka da IS da al-Qaeda.

    To amma kungiyoyin farar hula na cewa ga alama gwamnati na rufa-rufa kan zarge-zargen tare da kokarin kare wadanda ake zargi.

    Don haka kungiyoyin fafutikar ke matsa wa gwamnati lamba ta gurfanar da jami’an gwamnati da ke da hannu a lamarin na wawure kudaden tsaron.

    An dai fito zanga-zangar a Yamai babban birnin kasar amma ‘yan sanda sun toshe hanyoyin da masu zanga-zangar ke kokarin bi sannan suka tarwatsa masu zanga-zangar.

    Wasu rahotanni na cewa an samu asarar rayuka da jikkata a lamarin.

  17. Yadda 'yan kwana-kwana ke fama wajen kashe gobara a Legas

  18. Kungiyar Izala ta gudanar da taro a Abuja

    Kungiyar Izala a Najeriya ta gudanar da babban taronta na wa'azi da neman taimako na shekara-shekara a Abuja.

    Jigon taron na wannan shekara shi ne batun tsaro da na ilmi a kasa.

  19. Bidiyo: Isowar kwamishinan 'yan sanda na jihar Legas

  20. Bidiyo: Sojoji sun aiko da motar kashe gobara

    Rundunar Sojin ruwa ta Najeriya reshen jihar Legas ta aika da motar kashe gobara domin taimakawa wajen kashe gobarar da ta tashi sakamakon bututun mai da ake zargin ya fashe.