Yadda aka kashe ƴan sanda 13 a jihar Zamfara

Police

Asalin hoton, Getty Images

Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar jami'anta 13 a ƙauyen Kurar Mota na Karamar Hukumar Bungudu a jihar da ke arewa maso yammacin Najeriya

Rundunar ta tabbatar da faruwar lamarin ne a wata sanarwa da ta fitar wa manema labarar a ranar Lahadi, inda take cewa kisan jami'an ƴan sandan ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 12.30 na dare.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da jami'an suka amsa kiran kai daukin gaggawa kan yunƙurin kai farmaki a ƙauyukan da ke kusa a yankin karamar hukumar.

Sanarwar wacce kakakin rundunar 'yan sandan Mohammed Shehu ya fitar ta ce "Jami'an 'yan sanda 13 sun rasa rayukansu a bakin aiki, amma kuma su ma 'yan fashin dajin sun samu munanan raunuka".

Rundunar 'yan sandan jihar ta Zamfara ta yi alwashin cewa faruwar lamarain ba zai sanyaya gwuiwar jami'anta wajen gudanar da aikinsu na kare rayuka da dukiyoyin jama'a ba," in ji sanarwar.

Ta kuma yi kira fa duk wani dan kasa bai bin doka da su bai wa jami'an tsaro hadin kai wajen tabbatar da samun nasarar kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi jihar.

Da farko dai in ji mazauna yankin da suka shaida wa manema labarai, 'yan bindigar sun yi yunƙurin kai farmaki a ƙauyen Magami, mai nisan kilomita 50 daga kudancin Gusau babban birnin jihar amma sojoji suka fatattake su.

"Amma kuma sun abka wa wani ƙauye da ke tsakanin hanyoyin ƙauyukan Magami da Dankurmi da kuma Dangulbu inda suka banka wa shaguna huɗu wuta tare da hallaka mutum guda".

Daga nan ne suka abkawa ƙauyen na Kurar Mota inda suka kai hari kan caji ofis na 'yan sandan da ke kusa da dakin shan magani.

Wannan layi ne

Wasu labaran da za ku so ku karanta

Wannan layi ne

Ƴan sanda sun kashe ƴan fashin daji 10 a jihar Naija

A wani labarin daban kuma, ƴan fashin daji aƙalla 10 ne aka bayyana jami'an rundunar ƴan sandan jihar Neja da ke yankin tsakiyar Najeriya suka hallaka.

Lamarin ya faru ne a lokacin da suke ƙoƙarin daƙile kai wani hari a ƙauyen Kundu da ke Karamar Hukumar Rafi ta jihar a ranar Lahadi.

Gwamnan Neja

Asalin hoton, Niger Govt

Bayanan hoto, Gwamna Abubakar Sani Bello ya jajanta tare da jinjina wa jami'an ƴan sandan kan sadaukar da rai da kuma ƙoƙarin da suka nuna

'Yan fashin dajin dai sun yi kokarin kai munanan hare-hare a kan al'ummar ƙauyen na Kundu, a daidai lokacin rana ta ɓaci musu suka kuma gamu da ajalinsu.

A yayin da ya kai ziyara ƙauyen, gwamnan jihar Abubakar Sani Bello ya jajanta tare da jinjina wa jami'an ƴan sandan kan sadaukar da rai da kuma ƙoƙarin da suka nuna.

Gwamna Bello ya kuma jaddada yunkurin gwamnatin na tallafawa jami'an wajen ganin sun samu nasarar kare rayukan jama'ar jihar.

Wannan layi ne