Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Rawar da mata za su taka wajen yaki da cutar kwalara
Latsa hoton da ke sama domin sauraren shirin:
Mata kasancewarsu jagorori wajen kula da iyali za su iya yaki da cutar ne ta hanyar tsafatace muhalli da jiki da abinci da kwanukan abinci.
Haka kuma ilmantar da mata kan alamomin cutar da yadda za su kare kansu da iyali da yawan wanke hannu zai taimaka gaya, a cewar likitoci.
Cutar kwalara ta fi kamari a jikin yara saboda kashi 70 cikin dari na jikinsu ruwa ne.
Kimanin jihohi 14 ne cutar kwalara ta fi shafa a Najeriya, kuma akasarinsu na arewacin kasar.
Kasashe uku da cutar ta fi addaba a duniya sune Yemen da Indiya da kuma Jamhuriyyar Dimokradiyar Congo.
Alamomin cutar dai sun hada da zawo matuka da kuma amai a wasu lokuta.
Idan kuma ta yi kamari ta kan shafi koda ta kuma karar da sinadaren da ke jiki, inda ta kan kai ga asarar rayuka.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce a duk shekera kimanin mutane 1.3 zuwa miliyan hudu ne ke kamuwa da cutar amai da gudawar.
Haka kuma ana samu mutuwar mutane 21,000 zuwa 143,000 a fadin duniya.
Wasu daga cikin manyan dalilan da ke haddasa kwalara sun hada da rashin wadatar ruwa mai kyau da rashin tsaftataccen makewayi da rashin kyakkyawan tsarin kwashe shara da kuma cin abinci ko shan ruwan da ya gurbata da kwayar cutar.