Masana kimiyya na hasashen ɓarkewar annobar kwalara daga sararin samaniya

Masu bincike sun samo wata hanyar hasashen yaɗuwar annobar kwalara ta hanyoyin amfani da tauraron ɗan adam na sauyin yanayi da kuma basirar na'ura wato (artificial intelligence).

Masu binciken suna fatan wannan zai kare rayukan mutane a yankunan da suka fi fama da annobar.

"Abu ne mai kyau ƙwarai da gaske saboda yanzu za mu iya kula da duniyarmu," in ji Dr Paolo Cipollini, na hukumar kula da sararin samaniya ta Turai (ESA).

"Ba za ka taɓa tunanin sararin samaniya da tauraron ɗan adam za su iya magance matsalolin kiwon lafiya ba amma wannan wani abu ne da yake samun karɓuwa sosai."

Binciken ya nuna yadda samun ɓarkewar cutar kwalara a yankunan gaɓar Tekun Indiya da za a iya hasashe da kashi 89.

Tawagar ESA da kuma masu bincike na PML sun tattara bayanai na tsawon shekaru takwas daga taurarorin ɗan adam kan muhalli, kuma ta amfani da basirar na'ura da kuma ƙirƙirar hanyar da za a iya hasashen inda kwalera za ta iya ɓarkewa.

Cutar kwalara cuta ce da ake samu ta hanyar cin gurɓataccen abinci ko ruwa da ɗauke da kwayar cuta ta Vibrio Cholerae.

An fi samun masu cutar a kasashen da ke iyaka da arewacin Tekun Indiya, ciki har da Indiya, inda masu binciken suka mayar da hankali.

Sun yi amfani da ma'auni daban-daban guda bakwai daga tauraron dan adam wajen yin hasashensu.

Masana kimiya sun duba sauye-sauye a ruwa masu ɗanɗanon gishiri, inda ake samun ƙwayoyin cuta, da kuma ƙaruwar babbar ƙwayar cutar.

Sun kuma auna abubuwa kamar tururin zafi, inda mutane ke hutawa a bakin ruwa, ko ruwan sama, wanda zai iya haɗuwa da gurɓataccen ruwa mara tsafta.

"Abin da bincikenmu ya sha bamban shi ne yin amfani da irin dubaru daban daban," in ji mai bincike Amy Campbell, wacce ta yi aiki tare da ESA da PML wajen yin hasashen.

"Ɗaya daga cikin hanyoyin shi ne ɗanɗanon gishiri a ruwa, wanda sabon abu ne da ke da matuƙar taimakawa wajen hasashen yiyuwar ɓarkewar cutar kwalara.

"Idan har za mu iya amfani da shi don fahimtar lokacin da muke tunanin ɓarkewar cutar kwalara, za mu iya tabbatar da cewa an yi shiri, kuma za a iya rage cutar ta hanyar rigakafi a yankunan da cutar ta ɓarke."

Ɓarkewar annoba

Masana sun ce sauyin yanayi da yanayin zafi ke ƙara haifar da annobar kwalara.

Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) ta ce duk shekara ana samun mutum sama da miliyan huɗu da masu fama da kwalara, kuma mutum 143,000 ke mutuwa sanadiyyar cutar.

Duk da mutane kan nuna alamomin cutar, tana haifar da gudawa mai tsanani kuma cutar na iya kisa cikin lokaci ƙanƙani idan ba a yi gaggawar ɗaukar mataki ba.

"Ta fi shafar ƙananan yara waɗanda suka fi kamuwa da cutukan da ake samu da daga ruwa, yawancinsu ƴan ƙasa da shekara biyar.

"Muna fatan samun wannan da inganta hasashen yiyuwar ɓarkewar annobar korona zai taimaka wajen rage barazanarta ga yara," in ji Dr Marie-Fanny Racault, babban masanin kimiya na cibiyar bincike ta PML.

Masana kimiyya sun gano cewa hasashen zai kasance hanyar da za yi dogaro da musamman lokacin damina, da kusan kashi 93.3 cikin 100. Amma sun ce ana buƙatar ingantawa don ƙara tabbatarwa.