Gwamnatin Najeriya ta gargadi tsagerun Niger Delta kan barazanar kai hare-hare

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani game da barazanar da ƙungiyar tsagerun Neja Delta ta yi na ci gaba da kai hare-hare a kan harkokin aikin haƙar man fetur na ƙasar da ma wasu 'yan siyasar yankin.
Wannan barazana dai na zuwa ne jim kaɗan bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa da dattijan yankin Neja Delta a ƙarshen makon jiya kan matsalolin da suke ikirarin suna addabar yankinsu.
Malam Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaba Buhari ya bayyana wa BBC cewa akwai abin mamaki a barazanar da tsagerun suke yi ganin yadda shugaban ƙasar ya gana da shugabannin yankin tare da sauraron koke-kokensu.
A cewarsa, babu wani dalili da zai sa ita ƙungiyar ta fito tana barazanar ci gaba da kai hare-hare a yankin mai arzikin man fetur.
Malam Garba Shehu ya kuma yi ƙarin bayani game da wasu daga cikin alƙawuran da gwamnati ta yi waɗanda suka hada da batun hukumar raya yankin Neja Delta NDDC wadda ba ta da shugabancin hukumar daraktoci da manajoji.
"Shugaba Buhari ya ce a wata mai zuwa za a karɓi sakamakon bincike na kuɗaɗe da aka shigar da su wannan wuri yayin da ya kaɓi rahoto na ofisoshi da suka yi bincike na kuɗi zai kafa hukumar daraktoci da manajoji na wannan wuri". in ji Garba Shehu.
Haka nan a cewar Garba Sheuhu, jagororin yankin na Neja Delta sun bayyana buƙatar a ware musu rijiyoyin mai sai dai Shugaba Buhari ya ce akwai ƙa'idojin da ake bi wajen yin hakan duk da cewa akwai sassauci ga mazauna yankin.
Mai magana da yawun shugaban kasar ya kara da cewa babban abin takaicin shi ne duk ɓarnar da kungiyar tsagerun ke yi yana komawa ne a kansu.
Ya bayyana cewa "Idan kuka ɓarar da man fetur ɗin nan gonakinku zai shiga ya kashe tsirrai, zai shiga ruwa ya kashe kifi, kifin da kuma ba a kashe shi ba ya ƙara nisa ya shiga teku, don haka kanku kuke yi wa".
Malam Garba Shehu ya sanar da cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar mataki kan masu tada zaune tsaye a ƙasar.
"Hukuma da take da ƙarfi na tabbatar da cewa an kare tsarin mulki da dokoki na ƙasa, ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba, ba abin da zai hana cewa gwamnati, idan ya zama dole ta nemi ɗaukar mataki don kawo zaman lafiya a wuraren" in ji shi.











