Yadda ƴan bindiga suka hana arewacin Najeriya sakat
Latsa hoton sama sama domin kallon bidiyon
Masu garkuwa da mutane sun sace dalibai sama da 1,000 da malamansu a hare-hare daban-daban da suka kai makarantunsu a fadin arewacin Najeriya tun daga watan Disamban da ya wuce.
Matsalar garkuwa da mutane ta ta’azzara mawuyacin halin da fannin ilimin kasar yake ciki, inda da ma Najeriya ce kasar da aka fi samun yawan kananan yaran da ba sa zuwa makaranta a fadin duniya.