Shin ƴan bindiga sun zama hukuma ne a wasu kauyukan arewacin Najeriya?
Latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraren rahoton Abdussalam Ibrahim Ahmed:
Matsalar tsaro da ta addabi yankin arewacin Najeriya na ƙara ƙamari inda al'ummar wasu ƙauyuka suka shiga tsaka mai wuya.
Harajin da ƴan bindiga ke aza wa jama'ar wasu ƙauyuka musamman a arewa maso yammaci ya ƙara fito da girman matsalar tsaro a Najeriya.
Ƴan bindiga masu fashin daji musamman a Zamfara da Katsina da wani yanki na Kaduna sun ɓullo da sabon salo inda suke awon gaba da amfanin gona tare da kuma aza harajin girbi ga manoma.
A ranar asabar ne kuma ƙungiyar Boko Haram ta yi wa manoma yankan rago a yayin da suke aikin girbin shinkafa a kusa da garin Zabarmari a jihar Borno.
Wannan yanayi na matsalar tsaro ya sa manoma da dama sun haƙura da gonakinsu, lamarin da kuma ake ganin zai haifar da ƙarancin abinci a Najeriya.
Ikon ƴan bindiga

Asalin hoton, @DefenceInfoNG
Wasu mazauna kauyukan Zamfara sun ce 'yan bindigar na karbe musu miliyoyin kudi a matsayin haraji kafin su bari su ciri amfanin gonarsu
Kuma duk da kafa ikon na ƴan bindiga ba su dakatar da kai musu hari ba.
A farkon watan Nuwamba wani mazauni ƙauyen ɗan ƙurmi a ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara ya shaida wa BBC cewa ƴan bindigar sun aza masu kudi N800,000 a matsayin haraji kafin su bari su aikin amfanin gonarsu.
"Akwai kauyuka makwabtanmu irin su Duhuwar Saulawa, Duhuwar Maikulungu, Bauɗi, Zagadi, Doka da Tungar Makeri; wadannan kauyukan babu inda ba su aza wa mutane kuɗi ba kuma sun biya.
Bayan sun biya kudin kuma idan suka je aikin [gona] sai ƴan bindiga su ɗauke su," in ji shi.
Wani mazauni yankin kuma ya ce amfanin gonar shi ƴan bindigar suka kwashe gaba ɗaya.
"Bayan sun gama aiki an ɗinke sai 'yan bindigar nan suka kori manoman suka yi awon gaba da waɗannan kayan noman da suka cira."
A cewar waɗannan manoma, 'yan bindigar sun raba su da kayan amfanin gona na miliyoyin naira sannan ba su cika alkawarin da suka ɗauka na kin sace su ba.
Hakan ya sa suna kwana kullum ido ɗaya a buɗe sannan sun talauce domin kuwa an kwace kayan amfanin gonarsu da kuma 'yan kuɗaɗen da ke hannayensu.
"Ka ga irin su Duhuwa Saulawa sun biya kudin fiye da naira dubu ɗari uku amma duk da haka dajin ya kasa shiguwa. Yanzu wake idan ka shiga gonakinmu ga shi nan fari tas a kasa, shinkafa kuma ta ƙanbule tana son yanka amma babu dama," in ji shi.
Mazauna ƙauyukan sun ce wannan halin ya ƙara jefa su cikin talauci, "ba noma ba kiwo."
Me hukumomi suka ce?
Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce tana iya bakin ƙoƙarinta, kuma za ta ci gaba da bayar da tsaro na musamman.
Kakakin rundunar na jihar Zamfara SP Mohammaed Shehu ya yi kira ga mazauna ƙauyukan su daina bayar da haraji ga 'yan bindigar yana mai cewa yin hakan zai ƙarfafa masu gwiwar ci gaba da kai musu hare-hare.
Sai dai mutanen ƙayukan sun ce babu yadda za su yi su daina biyan haraji ga ƴan bindigar ganin cewa gwamnati ta kasa kare rayukansu da dukiyoyinsu.
A baya, gwamnatin jihar ta Zamfara ta ce ta yi sulhu da 'yan bindiga masu fashin daji domin su daina kai hare-hare amma kuma har yanzu sai ƙara ƙamari take.












