Rashin tsaro: Akwai yiwuwar a ci gaba da ta'addanci a Najeriya nan da shekara 20 – Buratai

Asalin hoton, TWITTER/@HQNIGERIANARMY
Shugaban hafsan sojojin ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya bayyana cewa akwai yiwuwar a ci gaba da samun ayyuka na ta'addanci a Najeriya har nan da shekara 20.
A wani saƙo da Buratai ɗin ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa: "Akwai ƙarancin fahimta kan abin da ta'ddanci ke nufi. Akwai yiwuwar a ci gaba da ta'addanci a Najeriya har nan da shekara 20."
Sai dai a cewar Buratai ɗin, "hakan zai iya ta'allaƙa ne kan irin ƙaruwar ta'addancin da ake samu da kuma irin gudunmowar daƙile ta'addanci da masu ruwa da tsaki ke bayarwa a ɓangaren farar hula da dakarun soji. Haka da gwamnatocin cikin gida da na waje".
Haka kuma ya yi kira ga jama'ar ƙasar da su bayar da haɗin kai wurin kawo ƙarshen rashin tsaro.

Wannan kalaman na Buratai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da aka yi wa manoman shinkafa 43 yankan rago a Zabarmari da ke jihar Borno.
Me masana tsaro ke cewa?
BBC ta tuntuɓi masanin tsaro, Barista Bulama Bukarti kan waɗannan kalamai na Buratai, inda ya bayyana cewa "waɗannan kalaman da Buratai ya faɗa ba su da daɗin ji amma ita ce gaskiyar magana".
A cewarsa, "yaƙin sunƙuru yaƙi ne wanda shi maƙiyinka ba zai zo ku yi gaba da gaba da shi ba, yaƙi ne mai sarƙaƙiya kuma ba a fara shi yau a gama shi gobe".
Sai dai a cewarsa, shekarun da Buratai ɗin ya kira wato kusan shekara 20 ya yi yawa, domin za a iya rage musu ƙarfi matuƙa a lokacin da bai kai wannan ba.
Ya kuma bayyana cewa duka yaƙin sunƙuru a duniya babban matakin da ake ɗauka shi ne na kare fararen hula.
"Duk sojin duniya idan suna yaƙin sunƙuru, babban matakin da ake ɗauka shi ne su kange garuruwa da ƙauyuka da gonaki su tabbatar da cewa ba a kai musu hari ba, kuma ɗaukar wannan mataki shi ne gwamantin Najeriya ta gaza"
Barrista Bukarti ya bayyana cewa tun farko gwamnatin Najeriya ba ta fito ta shaida wa 'yan Najeriya yadda ake yaƙin sunƙuru ba, "da sun gaya wa 'yan Najeriya gaskiya tun da wuri da shugaban ƙasa bai fito ya ce an gama da Boko Haram ba, da Buratai bai fito ya ce an doke Boko Haram ba, domin da aka yi maganar an doke su, sai aka ɗauka doke su ɗin abu ne mai sauƙi".
Bukarti ya bayyana cewa yanzu gwamnatin Najeriya ta fara fahimtar gaskiya kuma ya kamata su fara ɗaukar matakai na tabbatar da cewa an daƙile Boko Haram daga fararen hula

Asalin hoton, Getty Images
Sharhi
Yanayin rashin tsaro da Najeriya ke ciki na ci gaba da saka fargaba a zuƙatan 'yan ƙasar da kuma ɗaga hankulansu.
Tun bayan da matsalar tsaron ta ƙara ƙamari ake ta kira ga Shugaba Buhari ya sake fasali da sauya manyan hafsoshin tsaron ƙasar.
Amma da alama hakan ba lallai mai yiwuwa ba ne, domin shugaban ya nuna cewa yana gamsuwa da ayyukansu duk da kusan karo na biyu kenan da 'yan ƙasar ke kira da a sauke shugannin tsaron.
Ƴan Najeriya da dama na ganin lokaci ya yi da ya kamata shugaban ya sauke nauyi da alƙawuran da ya ɗauka na kare rayuka da dukiyoyi.
Fargabar zuwa gona na sake ƙaruwa tsakanin manoma, haka zalika harkokin kasuwanci na komawa baya saboda rashin kyawun hanya da tsoron masu satar mutane.
Masana harkokin tsaro na cewa idan ba a yi wa tufkar hanci tun da wuri ba, to ana iya wayar gari cikin gagarumar matsala da koma baya a fannin tattalin arziki da ƙarancin abinci.











