'Yan Kudancin Najeriya 'sun fi samun muƙamai a gwamnatin Buhari'

Buhari

Asalin hoton, Twitter/@Bashirahmad

Bayanan hoto, Arewa Maso Yamma ne yanki na biyu da ya fi samun mukamai a gwamnatin Buhari
Lokacin karatu: Minti 2

Bayanan da wani babban jami'in gwamnatin Muhammadu Buhari ya wallafa sun nuna cewa yankin Kudancin kasar ya fi samun mukamai a gwamnatinsa idan aka kwatanta da Arewacin kasar.

Bashir Ahmad, mai taimaka wa Shugaba Buhari kan shafukan zumunta, ya wallafa wasu alkaluma ranar Talata wadanda suka nuna cewa Kudancin Najeriya ya samu kashi 54.2 na mukaman da Shugaba Buhari ya raba tun da ya hau kan mulkin a shekarar 2015 zuwa watan Mayun 2020.

Arewacin kasar ya samu kashi 45.8 daga cikin dukkan mukaman da shugaban kasar ya raba.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Najeriya tana da yankuna shida: Arewa Maso Yamma, Arewa Maso Gabas, Arewa ta Tsakiya, Kudu Maso Kudu, Kudu Maso Yamma da kuma Kudu Maso Gabas.

'Yarbawa sun fi samun kaso mai tsoka'

Farefesa Osinbajo

Asalin hoton, Twitter/@akandeoj

Bayanan hoto, Yankin da Farfesa Osinbajo ya fito ya fi samun kaso mai tsoka a mukaman gwamnatin Buhari

Alkaluman sun nuna cewa a ciki wadannan yankuna, Kudu Maso Yamma, wato yankin Yarbawa inda mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ya fito, ya samu kashi mafi tsoka na mukamai a gwamnatin Buhari.

Yankin na Yarbawa ya samu 33.7 na mukaman da Shugaba Buhari ya nada.

Yankin Arewa Maso Yamma, inda Shugaban kasar ya fito shi ne na biyu rabon mukamai a gwamnatin ta Buhari inda ya samu kashi 19.5.

Sai kuma Arewa Maso Gabas mai fama da hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram, inda kusan daukacin hafsoshin tsaron kasar suka fito, wanda ya samu kashi 15.3.

Kudu Maso Gabashin Najeriya inda 'yan kabilar Igbo suka fi yawa shi ne kurar-baya a rabon mukaman da Shugaba Buhari ya yi inda ya samu kashi 7.9.

Da ma dai yankin ya dade yana korafin cewa an bar shi a baya wajen rabon mukamai a gwamnatin Shugaba Buhari, ko da yake galibin mazauna yankin sun ki zabar jam'iyyar APC mai mulki inda suka zabi jam'iyyar hamayya ta PDP.

Karin labaran da za ku so karantawa: