Mutum 10 ƴan gida ɗaya sun rasu bayan shan maganin gargajiya a Kwara

Ƴan sanda a jihar Kwara da ke yankin tsakiyar Najeriya sun ce mutum 10 ƴan gida ɗaya sun rasu sakamakon shan wani haɗi na maganin gargajiya.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata a ƙauyen Biogberu, a lokacin da wasu maza biyu da aka yi zarginsu da tunkarar wata mata da ke fama da wata cuta a ƙafarta, suka yi mata tayin maganin gargajiyar da zummar zai warkar da ita.

Amma sai suka bayar da sharaɗin cewa dukkan iyalan gidanta sai sun sha maganin don kare su daga kamuwa da cutar, wacce suka ce za ta iya yaɗuwa a tsakanin ƴan gidan.

Wani ɗan marigayiyar da ya kai ƙorafin gaban ƴan sanda ya ce mutanen sun kai wa mahaifiyarsa maganin ne ranar 18 ga watan Yunin nan.

Sannan mutanen gidan sun dinga rasuwar ne ɗaya bayan ɗaya.

A wata sanarwa, mai magana da yawun ƴan sandan jihar Kwara, Okasanmi Ajayi ya ce daga baya dukkan waɗanda suka sha maganin sun rasu.

Ya shaida wa BBC cewa "a ƙarshe da ita matar da sauran iyalan gidanta duk sun rasu."

Mista Ajayi ya ƙara da cewa mafi ƙarancin shekaru cikin waɗanda suka rasun yaro ne ɗan shekara biyu, yayin da mafi girma shi ne babba mai shekara 40.

Wasu labaran da za ku so ku karanta

Bincike

Ƴan sanda sun ce an kama waɗanda ake zargin biyu kuma ana ci gaba da bincike.

Har yanzu ba a tabbatar da cewa ko mutanen dama an san su da sayar da magungunan gargajiya ba a yankin.

Amma hukumomi sun ce nan gaba kaɗan za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.

Kwamishinan ƴan sandan jihar ya nemi mutane da su dinga zuwa asibitin da aka yi wa rijista a duk lokacin da ba su da lafiya maimakon shan magungunan da ake hada su da ka.

Ƴan Najeriya da dama musamman mazauna yankunan karkara sun dogara sosai kan amfani da magungunan gargajiya kan cututtuka da dama saboda ƙarancin ilimi da wayewa da imani da al'adu da kuma talauci.

Baya ga haka kuma taɓarɓarewar fannin lafiyar ƙasar na ƙara sa mutane son dogaro da magungunan gargajiya fiye da na asibiti.