Ebrahim Raisi: Tarihin mai tsattsauran ra'ayin da ya zama zaɓaɓɓen shugaban kasar Iran

Asalin hoton, ATTA KENARE/AFP
Ebrahim Raisi, mai tsattsauran ra'ayi kuma na hannun daman babban jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei, ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi makon da ya gabata.
Raisi, mai shekaru 60, ya gabatar da kansa a matsayin wanda ya fi cancanta ya yaƙi cin hanci da rashawa da kuma warware matsalar tattalin arziki da Iran ta sami kanta a ƙarƙashin Shugaba Hassan Rouhani mai barin gado.
Shi ne babban jojin Iran, wanda 'yan ƙasar da sauran masu rajin kare haƙƙin bil adama ke nuna wa ɗan yatsa kan rawar da ya taka wurin kisan fursunonin siyasa a shekarun 1980.

Asalin hoton, Anadolu Agency
An haifi Ebrahim Raisi a shekarar 1960 a Mashhad, birni na biyu mafi girma a Iran da ke da babban markazin mabiya Shi'a.
Mahaifinsa wanda shi ma malami ne ya mutu a lokacin Raisi na da shekaru biyar da haihuwa.
A ko da yaushe Mr Raisi ya kansa baƙin rawani wanda a Shi'a ke nuna cewa tsatso ne daga iyalin Annabi Muhammad (SAW).
Ya kuma bi sahun mahaifinsa inda ya shiga harkokin Shi'a gadan-gadan a birnin Qom tun yana ɗan shekara 15.
A lokacin da yake ɗalibta ya shiga zanga-zangar ƙin jinin Sarki Shah da ƙasashen Yamma ke goyon baya.
Kuma boren nasu ya yi nasarar tumbuke Sarkin a shekarar 1979 a juyin-juya halin da Ayatollah Ruhollah Khomeini ya jagoranta.
Iran ta zama Jamhuriyar Musulunci a shekarar 1979 a lokacin da Ayatollah Khomeini ya zama babban jagoran addini.

Asalin hoton, Getty Images
Tun bayan lokacin ne a ya fara aiki a ma'aikatar Shari'a a matsayin mai shigar da ƙara, inda a lokaci guda yake karɓar horo daga Ayatollah Khamenei wanda ya zama shugaban ƙasa a shekarar 1981.
Mr Raisi ya zama mataimakin mai shigar da ƙara a Tehran tun yana ɗan shekara 25.
Yana kuma riƙe da muƙamin ne ya shiga jerin alƙalai huɗu da suka gudanar da wani zaman shari'a cikin sirri a shekarar 1988 da aka yi wa laƙabi da 'kwamitin mutuwa'.
A zaman shari'ar ne aka gurfanar da dubban fursunonin siyasa, da dama daga cikinsu ƴaƴan ƙungiyar adawa ta Mujahedin-e Khalq da aka fi sani da People's Mujahedin Organisation of Iran (PMOI).

Asalin hoton, AFP
Har kawo yanzu babu ainihin adadin waɗanda aka yankewa hukuncin kisa a zaman shari'ar.
Amma a cewar ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama za su iya kai wa kusan mutun 4,000 da suka haɗa da mata da maza, kuma an binne su ne a manyan ƙaburbura da har yanzu babu wanda yasan inda suke.
Hakan ya sa ake zargin hukumomin Iran na lokacin da aikata kisan ƙare dangi.
Kuma shugabannin Iran ba su taba musa faruwar kisan ba, illa dai sun ƙi ba da gamsassar hujjar aikata hakan.
Mr Raisi bai taɓa bayyana rawar da ya taka ba a lokacin ba a bainar jama'a, amma kuma ya ce ya kafa hujja da cewa an yanke hukuncin ne bisa fatawar da Shugaba Khomeini ya bayar a lokacin.
Shekaru biyar da suka wuce wani sauti da aka nada tun a shekarar 1988 na taron da ya gudana na mambobin fannin Shari'ar Iran da suka hada da Mr Raisi, an ji mataimakin babban jagoran addinin a Iran na lokacin Ayatollah Hossein Ali Montazeri yana bayyana kisan fursunonin siyasar a matsayin babban ta'addancin da kasar ta taba aikatawa a tarihi.
Shekara ɗaya bayan haka Montazeri ya rasa kujerarsa a matsayin wanda zai gaji Khamenei, kuma bayan mutuwar jagoran addinin sai aka naɗa Ayatollah Ali Khamenei matsayin sabon jagoran addini a maimakon Montazeri.

Asalin hoton, Getty Images
Daga baya sai aka naɗa Mr Raisi a matsayin babban mai shigar da ƙara na Tehran, daga nan kuma ya riƙa samun ƙarin girma har ya kai babban mai shigar da ƙara na ƙasa baki ɗaya a shekarar 2014.
Bayan shekara biyu kuma sai Ayatollah Khamenei ya naɗa shi shugaban gidauniyar addini ta Astan-e-Quds-e Razavi da ke tara maƙudan kuɗaɗe.
A cewar Amurka gidauniyar na da hannayen jari a harkokin gine-gine da noma da makamashi da sadarwa da kuma hada-hadar kuɗaɗe.

Asalin hoton, AFP
A shekarar 2017 ne kwatsam Mr Raisi ya sanar da cewa zai tsaya takarar shugaban ƙasa.
Sai dai ya sha kaye a hannun Shugaban Hassan Rouhani wanda ya lashe wa'adi na biyu da kashi 57 cikin 100 na ƙuri'u.
Hakan bai sa tagomashin Mr Raisi ya dusashe ba, kuma a shekarar 2019 ne Ayatollah Khamenei ya zaɓe shi a matsayin Shugaban sashen Shari'a na Iran.

Asalin hoton, Anadolu Agency
Jim kaɗan bayan haka aka kuma naɗa shi mataimaki a kwamitin mutane 88 da ke zaɓar wanda zai zama babban jagoran addini.
A lokacin da yake shugaban sashen shari'a, Mr Raisi ya yi garambawul da ya sa aka rage adadin waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa da laifin kama su da ƙwaya.
Duk da haka Iran ce ta fi kowace ƙasa yanke hukuncin kisa bayan China.
Bugu da ƙari fannin shariar ya cigaba da aiki da hukumomin tsaro wurin kama Iraniyawa mazauna ƙasashen waje da kuma masu leƙen asiri.

Asalin hoton, EPA
A lokacin da Mr Raisi ya bayyana cewa zai yi takara a zaben shugaban ƙasa na shekarar 2021, ya ce ya tsaya ne a matsayin ɗan takara mai ƴanci, da zai yaƙi talauci, da cin hanci da rashawa, da cin zarafi da kuma nuna bambanci."
Sai dai jama'a basu san sirrin Mr Raisi ba sosai kan abin da ya shafi rayuwarsa da ta iyalinsa.
Illa dai matarsa Jamileh tana koyarwa a jami'ar Shahid Baheshti da ke Tehran, kuma suna da ƴaƴa biyu.
Surukinsa Ayatollah Ahmad Alamolhoda shi ma mai tsattsauran ra'ayi ne da ke jagorantar sallar Juma'a a garin Mashhad.










