Zaɓen Iran: Salon tsarin mulkin ƙasar na 'musamman'

Iranian Supreme Leader Ayatollah Ali Khamenei (3rd right), Quds Force chief Gen Esmail Qaani (2nd right), President Hassan Rouhani (4th right), judiciary chief Ebrahim Raisi (4th left), chairman of the Assembly of Experts Ahmad Jannati (R), attend a memorial for Qasem Soleimani in Tehran, Iran on 9 January 2020

Asalin hoton, Anadolu Agency

A wani tsarin siyasar ƙasar Iran na musamman, ana tafiyar da ƙasar bisa la'akari da tsari da tanadin addinin Musulunci da dimokuradiyya a tare.

Akwai wasu muhimman mutane waɗanda ba zaɓaɓɓu ba ne waɗanda suke aiki a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Addinin kasar inda yake aiki tare da zaɓaɓɓen Shugaban Kasa da 'yan majalisa da mutane ke zaɓa a lokaci bayan lokaci.

Ga yadda ake tafiyar da siyasar ƙasar a jere:

Shugaban Addini

Iranian Supreme Leader Ayatollah Ali Khamenei delivers a speech in Tehran, Iran (8 January 2021)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ayatollah Ali Khamenei ne Jagoran Addinin Iran tun 1989

Shi ne babban mai ƙarfin iko a Iran, wanda kuma tun bayan juyin juya halin kasar na shekarar 1979, sau biyu kawai aka yi, su ne Ayatollah Ruhollah Khomeini wanda shi ne ya assasa tsarin tafiyar da siyasar ƙasar a haka.

Sai wanda ya gaje shi wanda shi ne har yanzu Ayatollah Ali Khamenei.

Khomeini ne ya tsara tafiyar da kasar a haka ta yadda Shugaban Addinin zai fi sauran zaɓaɓɓun ƙarfin iko bayan an kifar da mulkin Shah Mohammed Reza Pahlavi.

Shugaban Addinin shi ne Babban Hafsan Dakarun Kasar, kuma harkokin tsaro na ƙarƙashin kulawarsa ne.

Shi ne yake da alhakin zaɓar Shugaban Bangaren Shari'a da rabin 'yan Majalisar Kula wadanda suna da ƙarfin iko matuƙa, da limaman Juma'a da kuma shugabannin gidajen rediyo da talabijin.

Sannan gidauniyar Shugaban Addinin, wadda take da biliyoyon daloli tana da matuƙar tasiri ga tattalin arzikin Iran ɗin.

Ayatollah Khamenei ya zama Shugaban Addinin ne bayan rasuwar Khomeini a 1989.

Ya yi ƙoƙari sosai wajen ci gaba daga inda Khamenei ya tsaya kuma ya yi ƙoƙari wajen rage musu ƙarfin adawa.

Shugaban Kasa

Iranian President Hassan Rouhani speaks at a cabinet meeting in Tehran (26 May 2021)

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Hassan Rouhani ya yi wa'adi biyu a matsayin shugaban ƙasa

Shugaban Kasa a Iran yana yin shekara hudu ne kuma yana da damar yin wa'adi biyu.

A Kundin Tsarin Mulkin Kasar, Shugaban Kasa ne na biyu a ƙarfin iko.

Shi ne shugaban ɓangaren zartarwa sannan shi ne ke da alhakin ɗabbaka Kundin Tsarin Mulkin Kasar.

Shugaban yana da iko a kan harkokin cikin gida da na waje, amma maganar Shugaban Addinin ce ƙarshe a duk abubuwan da suka shafi kasar.

A wannan watan ne mutanen Iran za su zaɓi shugaban da zai canji Hassan Rouhani, wanda malami ne mai matsakaicin ra'ayi wanda ya lashe zaɓukansa biyu ta hanyar yi wa abokan adawa kayin raba ni da yaro.

A duk zabukan guda biyu, yana lashe zaɓen da sama da kashi 50 na ƙuri'a wanda hakan ke sa wa ba sai an yi zagaye na biyu ba.

Duk dan takarar Shugaban Kasa sai ya tsallake tantancewa daga Majalisar Kula mai mutum 12, wanda ya kunshi lauyoyi da malamai.

A zaɓen wannan watan, a cikin 'yan takara 590 da suka nuna sha'awar takara, bakwai kawai kwamitin ta amince takararsu.

Majalisar Dokoki

Iranian President Hassan Rouhani speaks at a session of parliament in Tehran, Iran (3 September 2019)

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Majalisar tana da damar yin dokoki da amsa ko mayar da kasafin kuɗi sannan tana da ƙarfin iko gayyata tare da tsige minista ko ma Shugaban Kasa.

Duk bayan shekara hudu ne ake zaban mambobin majalisar da majalisa su 290 ta hanyar ƙuri'ar mutane.

Majalisar tana da damar yin dokoki da amsa ko mayar da kasafin kuɗi sannan tana da ƙarfin iko gayyata tare da tsige minista ko ma Shugaban Kasa.

Sai dai duk dokar da majalisar ta yi sai Kwamitin Kula ta musamman ta duba tare da amincewa.

A zaɓen 2020 masu ra'ayin rikau ne suka samu mafiya rinjaye bayan Kwamitin Kular ta ƙi amincewa da sama da 'yan takara 7,000 wadanda mafiya yawansu masu saukin ra'ayi ne da masu son kawo sauyi.

Kwamitin Kula

Ahmad Jannati speaks in Tehran, Iran (12 March 2019)

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kwamitin ya haɗa da masu tsaurin ra'ayi da suka haɗa da shugabansa Ayatollah Ahmad Jannati.

Kwamitin Kula ne kwamiti mafi karfi a Iran., aikinsa shi ne amincewa ƙuduran da aka gabatar a majalisar dokoki kuna yana da ƙarfin yin watsi da su. Zai kuma iya hana ƴan takara tsayawa a zaɓukan majalisar dokoki, da na shugaban ƙasa da na majalisar ƙwararru.

Majalisar ta haɗa masana addini shida da Jagoran Addini ya naɗa da kuma alƙalai shida da ɓangaren shari'a ya zaɓa kuma majalisa ta amince da su. Ana zaɓar mambobin ne tsawon shekara shida ta yadda ake sauya su duk bayan shekara uku.

Kwamitin ya haɗa da masu tsaurin ra'ayi da suka haɗa da shugabansa Ayatollah Ahmad Jannati.

Majalisar Kwararru

Meeting of the Assembly of Experts in Tehran, Iran (4 March 2014)

Asalin hoton, Anadolu Agency

Bayanan hoto, Ana yin zaben mambobin majalisar ce kai tsaye bayan shekara takwas

Majalisar Kwararru mai mutun 88 ta ƙunshi malamai ne kuma aikinsu ne zaɓan Shugaban Addinin da kuma lura da ayyukansa.

Sannan idan ya gaza suna da ikon cire shi.

Duk da cewa ba a taba samun inda ake ce an cire Shugaban Addinin ba, majalisar tana da matukar muhimmanci kuma yanzu hankali ya fara komawa kansu musamman duba da yanayin lafiya da shekarun Shugaban Addinin ya yanzu Ayotallhu Ayatollah Ali Khamenei wanda a yanzu ya kai shekera 82.

Idan Shugaban Addinin ya rasu ko kuma ya zama ba zai iya mulkin ba, majalisar za ta zauna ta yi zaben sirri ta zabo wanda zai maye gurbinsa.

Ana yin zaben mambobin majalisar ce kai tsaye bayan shekara takwas.

Zabensu na karshe ya wakana ne a 2016, inda nasu saukin ra'ayi kuma masu son kawo sauyi suka lashe kusan kashi 60 na kujerun bayan sun kasance masu rike da kasa da kashi 25 kafin wannan.

Shugaban majalisar na yanzu shi ne Ayatollah Ahmad Jannti wanda mai ra'ayin rikau ne kuma shi ne Shugaban Majalisar Kula.

Majalisar Masu Bada Shawara

Wannan majalisar aikinta shi ne ba Shugaban Addinin shawara sannan tana da ikon shiga tsakanin idan aka samu sabani tsakanin majalisar dokoki da Majalisar Kula.

Shugaban Addinin ne yake zaban mambobin majalisar guda 45 wadanda malamai ne da kuma jagororin al'umma. Shugabansu ya yanzu shi ne Ayatollah Sadeq Amoli Larijani, wanda shi ma mai ra'ayin rikau ne kuma ya taba zama shugaban bangaren shara'a.

Babban Alkali

Iran's judiciary chief Ebrahim Raisi speaks to reporters after registering as a candidate for the 2021 presidential election (15 May 2021)

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ebrahim Raisi ne shugaban bangaren shari'a tun shekarar 2019

Shugaban Addinin ne yake da ikon zaban Babban Alkalin kasar kuma a karkashinsa yake.

Babban Alkalin ne shugaban bangaren shara'a na kasar wanda kotuna da alkalai suke karkashinsa kuma suke aiki domin tabbatar da shara'ar Musulunci.

Babban Alkalin wanda a yanzu Ebrahim Raisi ne wanda shi ma mai ra'ayin riƙau ne, shi ne yake da alhakin zaban mambobin Majalisar Kula guda shida.

Bangaren shari'a tare da hadin gwiwar jami'an tsaro da jami'an tsaro na sirri suna aiki tukuru wajen tabbatar da bin dokar kasar, wanda hakan ya sa ake yawan zarginsu da tauye hakkin dan Adam.

Masu zabe

Women cast their votes at a polling station in Tehran, Iran, during parliamentary elections (20 February 2020)

Asalin hoton, AFP

A cikin mutanen kasar Iran guda miliyan 83, kusan miliyan 58 wadanda sun wuce shekara 18 sun isa su yi zabe.

Matasa sun fi yawa a cikin masu zaban, inda kusan rabin mutanen kasar matasa ne 'yan kasa da shekara 30.

A lokutan zabe, akan samu sama da kashi 50 sun kada kuri'a tun bayan juyin juya hali na 1979 sai dai a zaban majalisa na 2020, inda mutane da dama ba su fito ba saboda matsin tattalin arziki da korafe-korafen da ake yi a lokacin na mulkin Addinin Musulunci a Kasar.

Rundunar tsaro

Iranian President Hassan Rouhani attends military parade on National Army Day in Tehran, Iran (18 April 2019)

Asalin hoton, Anadolu Agency

Bayanan hoto, Rundunar Tsaron kasar ta kunshi Rundunar Juyin Juya Hali na Musulunci wato Islamic Revolution Guard Corps (IRGC) da kuma sojoji

Rundunar Tsaron kasar ta kunshi Rundunar Juyin Juya Hali na Musulunci wato Islamic Revolution Guard Corps (IRGC) da kuma sojoji.

An kafa IRGC ce bayan juyin juya halin da aka yi a kasar domin tsarewa tare da tabbatar tsarin siyasar kasar ta Musulunci da kuma taimakon sojojin.

Rundunar tana da karfin makamai kuma tana da karfin iko akan siyasa da tattalin arzikin kasar. Ita ma tana karkashin kukawar Shugaban Addinin ne.

A rundunar akwai sojan kasa da na ruwa da na zama sannan ita ce ke da alhakin kula da makaman kasar.

Sannan ɓangaren tsaron harkokin cikin gida na karkashinta ne wanda suke taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da doka a cikin kasar.

Shugaban Addinin ne yake da alhakin zaban manyan hafsoshin rundunar kuma suna karkashinsa ne kawai.

Majalisar Zartarwa

Iranian President Hassan Rouhani chairs a cabinet meeting in Tehran, Iran (8 January 2020)

Asalin hoton, Anadolu Agency

Bayanan hoto, Shugaban Kasa ne yake zaban mambobin Majalisar Zartarwa

Shugaban Kasa ne yake zaban mambobin Majalisar Zartarwa.

Sai dai dole majalisa ta tantance tare da tabbatarbda su kuma majalisar za ta iya cire minista.

Shugaban Kasa ko Mataimakin Shugaban Kasa ne ke shugabantar Majalisar Zartarwa.a.