Idriss Deby: Waiwaye kan rayuwar marigayi tsohon shugaban Chadi a cikin hotuna

Wasu daga cikin hotunan rayuwar marigayin shugaban kasar Chadi Idris Deby Itno.

Shugaban Chadi Idriss Deby tare da maidakinsa Hinda Deby Itno a lokacin da suka halarci liyafar cin abincin dare ta fadar shugaban kasa, da kai ziyara baje koli Picasso a wani bangare na bikin cika shekara 100 da kawo karshen yakin duniya na farko, wato 11 Nuwamba 1918.

Asalin hoton, Hoto daga Mehdi Taamallah da Getty Image

Bayanan hoto, Shugaban Chadi Idriss Deby tare da maidakinsa Hinda Deby Itno a lokacin da suka halarci liyafar cin abincin dare ta fadar shugaban kasa, da kai ziyara baje koli Picasso a wani bangare na bikin cika shekara 100 da kawo karshen yakin duniya na farko, wato 11 Nuwamba 1918.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (hagu) da shugaban Chadi Idris Deby (hagu) su na ganawa a lokacin taron shugabannin kasashen yankin Sahel da Sahara (CEN-SAD) a ranar 13 ga watan Afirilu 2019 a birnin N'Djamena.

Asalin hoton, Hoto daga Ibrahim ADJI/AFP da Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (hagu) da shugaban Chadi Idris Deby (hagu) suna ganawa a lokacin taron shugabannin kasashen yankin Sahel da Sahara (CEN-SAD) a ranar 13 ga watan Afirilu 2019 a birnin N'Djamena.
Shugaban Chadi Idriss Deby Itno (Hagu) ya karbi bakuncin takwaransa na Najeriya Goodluck Jonathan a filin jirgin sama na birnin N'Djamena's a ranar 8 ga watan Satumba 2014. Shugabannin biyu za kuma su tattauna kan yarjejeniyar yin aiki tare domin magance matsalar masu tada kayar baya da ayyukan ta'addanci wanda kasashen Najeriya da Chadi da Nijar da Kamaru suka rattabawa hannu a birnin Paris na kasar Faransa a wannan shekarar.

Asalin hoton, Hoto daga Ibrahim ADJI/AFP tare da Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Chadi Idriss Deby Itno (Hagu) ya karbi bakuncin takwaransa na Najeriya Goodluck Jonathan a filin jirgin sama na birnin N'Djamena's a ranar 8 ga watan Satumba 2014. Shugabannin biyu kuma sun tattauna kan yarjejeniyar yin aiki tare domin magance matsalar masu ta da ayar baya da ayyukan ta'addanci wanda kasashen Najeriya da Chadi da Nijar da Kamaru suka rattabawa hannu a birnin Paris na kasar Faransa a wannan shekarar.
Idriss Deby

Asalin hoton, TWITTER/IDRISS DÉBY ITNO

Bayanan hoto, A watan Yunin 2020 ne majalisar dokokin kasar ta Chadi ta amince da wata doka da ta kara wa shugaban kasar Idrissa Deby Itno girma daga Janar zuwa mukamin Marshal - wanda shi ne mukamin da ya fi kowanne a tsarin aikin soji.
Shugaban Chadi Idris Deby Itno, da maidakinsa Hinda Deby Itno a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban Fransa Nicolas Sarkozy da maidakinsa Carla Bruni-Sarkozy a filin jirgin sama na birnin N'Djamena, a ranar 27 ga watan Fabrairu 2008.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Chadi Idris Deby Itno, da maidakinsa Hinda Deby Itno a lokacin da ya karbi bakuncin tsohon shugaban Fransa Nicolas Sarkozy da maidakinsa Carla Bruni-Sarkozy a filin jirgin sama na birnin N'Djamena, a ranar 27 ga watan Fabrairu 2008.
PShugaban Nijar Muhammadou Issoufou tare da shugaban Chadi Idris Deby Itno a lokacin taron manema labarai, bayan kammala taron kasa da kasa a fadar Elysee da ke birnin Paris na kasar Faransa a ranar 28 ga watan Agusta 2017. A lokacin taron sun tattauna kan batutuwan siyasa da halin da ake ciki a Turai da batun tsaro a kasashen Turai.

Asalin hoton, Hoto daga Aurelien Meunier Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Nijar Muhammadou Issoufou tare da shugaban Chadi Idris Deby Itno a lokacin taron manema labarai, bayan kammala taron kasa da kasa a fadar Elysee da ke birnin Paris na kasar Faransa a ranar 28 ga watan Agusta 2017. A lokacin taron sun tattauna kan batutuwan siyasa da halin da ake ciki a Turai da batun tsaro a kasashen Turai.
Shugaban Chadi Idriss Deby Itno (Tsakiya) lokacin da ya kada kuri'a a mazabarsa da ke birnin N'djamena, a ranar 11, ga watan Afirilu 2021. - Al'ummar Chadi sun fita domin kada kuri'ar zaben shugaban kasa a ranar 11 ga watan Afirilun 2021 wanda Idriss Deby Itno, da ya mulki kasar na kusan shekaru 30 ya ke neman wa'adin mulki na shida.

Asalin hoton, Hoto daga Marco Lomgari/AFP da Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Chadi Idriss Deby Itno (Tsakiya) lokacin da ya kada kuri'a a mazabarsa da ke birnin N'djamena, a ranar 11, ga watan Afirilu 2021. - Al'ummar Chadi sun fita domin kada ƙuri'ar zaben shugaban kasa a ranar 11 ga watan Afirilun 2021 wanda Idriss Deby Itno, da ya mulki kasar na kusan shekaru 30 yake neman wa'adin mulki na shida.
Shugaba Emmanuel Macron (Dama) ya karbi bakuncin shugaban Chadi Idris Debby Itno (Hagu) a fadar Elysee a ranar 28 ga watan Agusta 2017 a birnin Paris na kasar Faransa. An shiry taron ne domin jaddada goyon bayan Turai ga Chadi a kokarin da ta ke yi da yaduwar tsuntsaye.

Asalin hoton, Hoto daga hristophe Morin/IP3/ Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Emmanuel Macron (Dama) ya karbi bakuncin shugaban Chadi Idris Debby Itno (Hagu) a fadar Elysee a ranar 28 ga watan Agusta 2017 a birnin Paris na kasar Faransa. An shirya taron ne domin jaddada goyon bayan Turai ga Chadi a kokarin da take yi da yaduwar tsuntsaye.
Shugaban Chadi Idriss Deby (Hagu) ya na magana da sojan (Dama) da ke kula da rundunar sojin da ke sansanin da suke aiki a tafkin Chadi a wajen Niamey ranar 24 ga watan Junairu, 2013, akan hansarsu ta zuwa kasar Mali. Kasar Chadi ta rubanya dakarunta a Nijar domin taimaka mata da yaki da mayakan jihadi da ke arewacin birnin Gao na kasar Mali, kamar yadda majiyar Chadi ta bayyana an kara dakaru 400 kan 200 da ake da su tun da fari. Kasashen Afurka sun zabura domin taimakawa Mali sai dai an samu matsalar kudaden sayan kayan aiki wanda hakan ya janyo koma baya a yakin da ake yi, kamar yadda jami'an diflomasiyya suka bayyana.

Asalin hoton, Hoto daga Boureima Hama/AFP da Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Chadi Idriss Deby (Hagu) yana magana da sojan (Dama) da ke kula da rundunar sojin da ke sansanin da suke aiki a tafkin Chadi a wajen Niamey ranar 24 ga watan Junairu, 2013, a kan hanyarsu ta zuwa kasar Mali. Kasar Chadi ta rubanya dakarunta a Nijar domin taimaka mata da yaki da mayakan jihadi da ke arewacin birnin Gao na kasar Mali, kamar yadda majiyar Chadi ta bayyana an kara dakaru 400 kan 200 da ake da su tun da fari. Kasashen Afurka sun zabura domin taimakawa Mali sai dai an samu matsalar kudaden sayan kayan aiki wanda hakan ya janyo koma baya a yakin da ake yi, kamar yadda jami'an diflomasiyya suka bayyana.