Matsalar tsaro : Najeriya ta fara kafa na'urorin sa ido a kan iyakokinta

Iyakar Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin Najeriya ta ce ta fara kafa wasu na'urorin sa ido a faɗin iyakokin ƙasar, don bunƙasa tsaro da daƙile fataucin makamai da ƙwaya har ma da mutane.

Hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ta ce matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin zamanantar da ayyukanta, tare da shigar da ɗumbin fasahohin sadarwa don inganta tsaron ƙasar.

Muhammad Babandede wanda shi ne babban kwanturolan hukumar shige da ficen, ya shaida wa BBC cewa matsalar tsaro na daya daga cikin dalilan da suka sanya aka dauki wannan mataki, da kuma aniyar hana shigo da makamai da kuma kwararar miyagu cikin Najeriya.

A cewarsa: ''Iyakarmu ta ƙasa ta fi fadi musamman iyakokinmu da Hamada, kamar kasar Nijar, fatanmu shi ne da zarar mun ga wani abu na ban tsoro mu sanar da ma'aikata ko sojan sama ko na kasa domin su ɗauki mataki idan mun ga ya fi karfinmu.''

Ya kara da cewa yanzu haka an fara sa na'urorin, kuma ana ganin abubuwan da ke faruwa, kuma nan gaba kadan Shugaba Muhammadu Buhari zai tabbatar da cewa an sanya wadannan naurori a dukkanin iyakokin Najeriya 86, wanda hakan zai magance matsaloli da dama da Najeriya ke fuskanta a halin da ake ciki.

Ya ce za a sanya na'urar ne a kan iyaka da kuma kan motoci da za su riƙa kewayawa, baya ga ɗaukar bayanan yatsun masu shiga ƙasar domin tabbatar da cewa masu shiga ƙasar ba mugaye ba ne.

Shi dai Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci yawancin ma'aikatan hukumar ta shige da fice su koma kan iyakokin Najeriya domin tabbatar da tsaro da kuma kare kwararar makamai.

Baya ga haka ministan cikin gida na Najeriya ya umarci hukumar ta matsa ƙaimi wajen aiwatar da rijistar zaunawa a Najeriya da zarar baƙo ya cika kwana 80 a ƙasar, hasalima yanzu an rage kwanakin zama kafin yin rijistar daga kwana 80 zuwa kwana 30, wato wata guda kenan.

Dama an jima ana zargin cewa maharan da ke kai hari a wasu jihohin Najeriya musamman na Arewa ba ƴan Najeriya ba ne, sukan shigo ne daga waje da muguwar aniya.

Shi kansa Shugaba Muhammadu Buhari ya taɓa yin zargin cewa ana shigo da makaman da ake kai hare-hare da su a ƙasar ne daga wasu kasashe da suka fuskanci yaƙi a baya, kamar Libiya.