Muhammed Babandede: Ba za a iya kawar da cin hanci lokaci ɗaya ba

- Marubuci, Haruna Kakangi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-media Broadcast Journalist
Shugaban hukumar shige-da-fice ta Najeriya Muhammad Babandede ya ce yana yin bakin kokarin sa wajen ganin an rage matsalar cin hanci a hukumar.
A cikin tattaunawa ta awa guda da BBC Hausa ta gudanar da shugaban hukumar, ya ce yana sane da korafe-korafen da mutane ke yi na cewa wasu jami'an hukumar na karbar kudi a hannun mutane a bakin iyakar kasar.
A cewar sa: "Ina so na sanar wa al'umma cewa duk wani shugaba kamar ni idan na ce ba a karbar cin hanci to ba gaskiya ba ne. Amma hakkinmu ne mu hana".
Ya kara da cewa cin hanci ya fi muni ne a idan ya kasance shugabanni suna karfafa wa na kasa da su gwiwa wajen ci gaba da aikatawa yana mai ikirarin cewa hakan na faruwa a lokutan baya, sai dai ya ce a yanzu yana kokari wurin ganin cewa an rage matsalar ta cin hanci.
Ya kuma ce zai kama duk wani kwanturola na hukumar da aka bayar da rahoton ana karbar cin hanci a yankin da yake lura da shi.
Sai dai a lokacin da aka tambaye shi ko yaushe za a kawo karshen cin hanci a tsakanin ma'aikatan hukumar? Muhammad Babandede ya ce za a samu saukin abin a yanzu amma ba za a iya kawar da shi gaba daya ba.

"Ni ina so ne na fada maka gaskiya ne, cin hanci cuta ce, ba yadda za a yi ka je Najeriya ko Amurka ko Ingila ka ce babu cuta, amma za a samu sauki, duk wanda aka kama za a hukunta shi," a cewarsa.
Tun farko dai a cikin shirin na A FADA A CIKA, wasu mutanen da ke zaune a bakin iyaka sun turo da korafi ne kan yadda jami'an hukumar ta shige-da-fice ke tursasa musu biyan kudade ba bisa ka'ida ba kafin shiga ko fita daga Najeriya.
Wani da ya aiko da sako ya ce: "Koda kai dan kasa ne, in dai ba ka tafi da katin dan kasa ba, ko ka manta shi a gida, sukan amshi kudi hannunka, ballantana ma 'yan Nijar, ba za a tambaye su ko sun cika sharuddan shiga ko fita daga kasar ba, (abinda suke nema shi ne) mene ne a cikin aljihunsa, mene ne abin da za su tatsa daga jikinsa. Hakika hakan yana zubar da kima da mutuncin gwamnati a idon talakawa."
Wani kuma ya ce: "Tun farko kafin a rufe boda (iyakar kasa) muna ba su kamar Naira 100 mu samu mu wuce, amma yanzu yanzu bayan rufe boda abin ya kai Naira 500, kai ya kai ga har ma da dukan jama'a suke yi.
Daya daga cikin wadanda suka halarci tattaunawar shi ne Sada Soli Jibiya, dan majalisar dokkin tarayya mai wakiltar Jibiya/Kaita, inda ya bukaci shugaban hukumar ta shige-da-fice da ya bincika abubuwan da ke faruwa a yankuna na bakin iyakar Najeriya.
A cewarsa ba cin hanci kawai ake yi ba, har ma da cin mutuncin mutane. "Ba ma cin hanci kawai ba, cin fuska ake yi. Cin fuska ake wa mutanenmu an mayar da su kamar ba 'yan Najeriya ba, ina son jami'in nan ya kara bincikawa ya ga cin hanci da ake yi wa 'yan kasa da baki," in ji shi.

Sai dai a lokacin da ya yi bayani, Muhammad Babandede ya bukaci mutane da su rinka shigar da korafinsu ga hukumar ta yadda za ta rinka hukunta masu laifi.
Ya kuma ce hukumar za ta mayar da hankali wajen sauraron koke-koken al'umma, musamman bayan korafe-korafen da ya saurara daga wadanda suka turo da sakonni.
A dangane da batun fasfo na tafiye-tafiye zuwa kasar waje kuwa shugaban hukumar ta shige-da-fice ya shawarci mutane da su rinka biyan kudin katin ta shafin intanet. A cewar sa hukumar ta kirkiro da wannan tsari ne domin rage mu'amala da kudi tsakanin mutane, ta yadda za a rage matsalar zarge-zarge na karbar cin hanci kafin samun takardar ta fasfo.











