Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda za a warware rikici tsakanin Fulani da Shugabannin Kudancin Najeriya
Manazarta kan al'amuran jama'a a Najeriya sun yi kira ga manyan ƴan ƙasa da suke jihohin Najeriyar da ka da su yi ƙasa a gwiwa wajen ƙulla yarjejeniyar sulhu da shugabannin kudancin ƙasar da Fulani makiyaya - wadanda a yanzu haka ake fitar da su daga dazukan da ke jihohin Kudancin ƙasar.
Dr. Muhammad Musa Maitokobi, mai sharhi kan al'amuran kasa ya faɗa wa BBC cewa tuntubar manyan ƙasa daga kudanci da arewacin Najeriya zai kai ga tabbatar da zaman lafiya da kaucewa sake afkawa cikin fitina ta yaƙi, kamar yadda wasu ke ta zuzutawa.
Wannan kiran ya zo ne a yayin da ake zargin akwai bata gari a cikin wasu daga Fulani makiyayan.
Yadda za a kamo bakin zaren
A cewar Dakta Maitokobi, abin da ya kamata a yi domin warware wannan matsala shi ne kai zuciya nesa saboda akwai shugabanni ba wai ana zaune kara zube bane.
"Akwai jihohi da shugabanninmu da gwamnoni ma wasu Fulani ne, don haka za su iya zama da shugabannin waɗan nan ƙasashe na Yarbawa a nemi maslaha, su kuma mutanenmu (Yarbawa) a nuna musu cewa
yin abin da suke yi ba shi ne zai kawo zaman lafiya a tsakanin juna ba".
Idan yau ka kashe ni ka kashe dukiya ta, toh a nan kana da ƙarfin ka yi haka, a wajen kuma da kai kuma kake da dukiyar kai ma ba ka da ƙarfi fa? Zama za a yi a nemi yadda za a tattauna a yi maganin abun". in ji Dakta Maitokobi.
Ya bayyana cewa akwai auratayya tsakanin duka ƙabilun a don haka bai kamata a ce ana samun rashin jituwa ba a tsakaninsu.
Mai sharhin ya ce idan har a zaman sulhun da aka yi ba a cimma wani ci gaba ba, hakan na nufin a ci gaba da tattaunawa har sai an samu maslaha.
Yana ƙara da cewa sanya manya a batun zai taka rawa sosai a wannan rikici da ake ta yi.
Zamanantar da harkar kiwo
Dr Muhammad Musa Maitokobi ya ce ci gaba ne ke sa a zamanantar da harkar kiwo "idan muma ci gaban ya zo da gaskiya da daidaituwa ta zo, kar ma ka gaya wa mutum, shi da kansa zai nemi wurin da zai killace dabbobinsa saboda ba ya son dabbobin su tafi ya rasa su".
Ya ba da misali da Saudiyya inda ya ce akwai makiyaya a ƙasar "amma za ka ga kowane wuri an killace an kewaye wurin, an kawo ciyawa an kawo abubuwan da dabbobin nan za su yi amfani da su, a wurin ake kiwonsu".
"Muma Najeriyar idan zamani ya zo da daidaituwar, za a wayi gari ka ga ba ka samu Bafulatani a daji ba, su kansu Fulanin a kashi 100, kashi 45 ko 50 ba shanunsu bane" saboda a cewarsa masu shanun suna birni sun sayi shanun, su suke musu wahala da shanun.