Taro kan Fulani: Sharuɗa biyar da aka gindaya wa makiyaya a kudu maso yammacin Najeriya

Gwamnonin jihohin kudu maso yammacin Najeriya da na arewaci sun cimma yarjejeniya game da zamantakewar Fulani a yankin kabilar Yarbawa.

Hakan ta faru ne bayan kammala taron da suka yi a Akure babban birnin jihar Ondo tare da kungiyar Miyetti-Allah ta Fulani makiyaya a ranar Litinin.

A yarjejeniyar wacce ke kunshi a bayanin bayan taron da suka fitar, duka bangarorin biyu sun amince da bukatu 13 da suka hada da wasu sharuda da aka gindaya wa Fulani makiyayan.

Sharudan su ne:

- A haramta yin kiwo cikin da dare daga yanzu.

- Haramta kananan yara fita kiwo, wanda aka bayyana cewa yana barazana ga harkokin tsaro.

- Mamaye dazukan gwamnati karya doka ne, don haka an hana wannan ma.

- Ya zama wajibi dukkan makiyaya su yi rijista

- Dole kungiyar Fulani makiyaya ta rungumi tsarin kiwo na zamani ta hanyar samar da matsugunai ga mambobinta tare da hana su yawo barkatai, don kauce wa rikici tsakanin manoma da makiyayan.

Mahalarta taron sun kuma yarda cewa matsalar tsaro babban kalubale ne da ya shafi kasa baki daya, ba kawai an ware wata kabila ko kuma wani yanki ba.

An gindaya wadannan sharuda ne bayan ce-ce-ku-cen da ya barke sakamakon wa'adin da gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu ya bai wa makiyaya su fice daga dazukan jiharsa.

Ya zargi "wasu bara-gurbi da ke fakewa da sunan makiyaya" suna aikata laifuka a jiharsa.

Kazalika an yi taron ne bayan wani dan bangar Yarbawa Cif Sunday Adeyemo wanda aka fi sani Igboho ya umarci makiyaya su fice daga jihar Oyo yana mai zargin su da hannu a satar mutane domin karbar kudin fansa da kuma wasu laifuka a jihar.

Sai dai makiyaya sun musanta dukkan wadannan zarge-zarge suna masu cewa kora-da-hali ake so a yi musu daga yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Taron ya kunshi gwamnonin jihohin arewacin Najeriyar da suka hada da Kebbi Abubakar Atiku Bagudu da Jigawa Badaru Abubakar da kuma takwarorinsu na kudu maso yamma da suka hada da Seyi Makinde na Oyo da Rotimi Akeredolu na Ondo da na Ekiti Kayode Fayemi da na Osun Gboyega Oyetola.

Burinsu shi ne a lalubo hanyoyin warware matsalolin sace-sacen jama'a domin neman kudin fansa, da rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin kudu maso yammacin kasar.