Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda rikicin Fulani zai shafi alakar arewa da kudu maso yammacin Najeriya
Abin da ya faru ga Fulani makiyaya a wasu jihohin shiyar kudu maso yammacin Najeriya ya fara jefa shakku kan makomar alaƙa tsakanin yankin da kuma na arewaci da Fulanin suka fito.
An yi tattaunawa a birnin Akure na jihar Ondo tsakanin gwamnonin kudu maso yammacin Najeriya da kuma shugabannin Fulani makiyaya a wani yunƙuri na lalubo bakin zaren warware zaman ɗar-ɗar da ake yi.
Tun bayan wa'adin korar makiyaya daga dazukan jihar Ondo da kuma wani wa'adin da aka ba Fulanin a jihar Oyo, Fulanin suka shiga zaman zullumin a jihohin Yarabawa a Najeriya.
Ko da yake Gwamnan Ondo ya ce kafofin yaɗa labarai sun yi wa umurnin da gwamnatinsa ta bayar muguwar fahimta inda ya ce ya bayar da umurni ne kawai ga makiyaya su fice da suka mamaye daji ba bisa ka'ida ba.
Ana fatan matsayar da aka cimma tsakanin gwamnonin kudu maso yammaci da na arewacin Najeriya da kuma shugabannin Fulani ta ɗore da samar da fahimtar juna da game da zaman Fulani a yankin ƙabilar Yarbawa.
Yadda matsalar ta faro
An fara sunsunar rikicin ne a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya, tun a watan jiya, bayan fitar wani hoton bidiyo da aka ce na wasu Fulani wadanda aka tarwatsa musu matsugunansu.
A cikin bidiyon akwai muryar wani da ke ikirarin cewa shi ɗan yankin ne, wanda yake cewa sun yanke shawarar fatattakar Fulanin ne saboda suna barazana ga tsaron yankin.
Wasu shugabannin Fulani sun nuna damuwa sosai game da lamarin inda suka buƙaci a gudanar da bincike, abin da suka ce an shiru.
Bayan wannan kuma an sake yi wa Fulanin gargaɗi a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya, inda wani mai jin isa, mai suna Sunday Igboho ya bai wa Fulani wa'adin su tattara nasu ya nasu su fita daga jihar Oyo, bisa zargin cewa suna ba masu satar mutane mafaka.
Kafin cikar wannan wa'adin ne gwamnan jihar Ondo ya fito kai-tsaye ya umurci Fulanin jihar da su yi gaba, kuma duk maganar ɗaya ce, wato zargin cewa suna barazana ga tsaro.
Tsawon faruwar wannan lamari, kamar yadda masu lura da al`'mura ke zargi, babu wani mataki a zahiri da mahukunta suka dauka har zuwa ranar juma`ar da ta gabata.
lokacin da wa'adin da aka ba Fulanin Iganga da ke jihar Oyo ya cika, kuma Sunday Igboho ya jagoranci wasu matasa suka far ma matsugunan Fulanin, inda suka ƙona gidaje da motoci da sauran ƙadarorinsu.
Wannan ya sa wasu ƙungiyoyi ciki har da masu kare muradan Yarabawa suka yi wani abu mai kama da fargar-jaji, wato suka yi tir da harin, wasu kuma na cewa a gudanar da bincike.
Ita gwamnatin Tarayya ta la'anci waɗanda suka ta da fitinar kuma rundunar `yan sanda ta yi iƙirarin kama wasu.
Illa ga ƙawancen siyasa tsakanin arewa da kudu masu yamma
An daɗe ana ƙawancen siyasa tsakanin arewa da kudu masu yammaci musamman wajen fafutikar neman shugabancin ƙasa.
Amma masu sharhi kamar Malam Kabiru Sufi masanin siyasa a Najeriya yana ganin abu mai ɗaure kai shi ne yadda manyan shugabannin al'umma, musamman ma jiga-jigan siyasar kudu maso yamman suka yi gum da bakinsu.
Kabiru Sufi ya ce irin haka wani ragon-azanci ne.
"Akwai waɗanda ake ganin cewa ya kamata a ce sun ɗau mataki tun abun bai kai haka ba amma ba su yi komai ba.
"Ya kamata a ce shugabannin siyasa na yankin sun fito sun tsawatar don a hana abin lalacewa," a cewarsa.
Duk da cewa wannan matsala ce da ta shafi tsaro, masana na cewa tana iya fantsama ta shafi dangantakar siyasa, musamman ma kawancen da ke tsakanin shiyyar kudu maso yamma da kuma arewacin Najeriya.
Malam Kabiru Sufi ya ce "A baya irin wannan ƙawancen ne ma ya kai ga nasarar wannan gwamnatin, akwai bukatar ganin cewa wannan ƙawance ya ɗore don a kai ga manufar da ake so a kai musamman a zaɓen 2023."
Masana dai na cewa an so a makara, amma ana fata matakin da gwamnonin yankin suka ɗauka tare da sauran masu ruwa da tsaki don samun mafita a kan lamarin, zai taimaka wajen tabbatar da tsaro da kuma gujewa tsamar dangantaka a tsakanin ɓangarorin biyu.