Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
EndSars: ‘Yan sanda sun lakaɗa wa masu zanga-zangar EndSars duka
'Yan sandan Najeriya sun lakada wa masu zanga-zangar EndSars duka sannan suka kama da dama daga cikinsu a Lagos, cibiyar kasuwancin kasar.
Masu zanga-zangar sun fito kan tituna ne domin nuna adawa da matakin da gwamnatin jihar Lagos ta dauka na sake bude hanyar Lekki toll gate.
Kwamitin jin bahasi da gwamnatin jihar ta kafa kan harbe-harben da wasu ƴan ƙasar suka ce sojoji sun yi wa masu zanga-zanga ranar 20 ga watan Oktobar 2020 ne ya amince da sake buɗe toll gate din.
Tun ranar Juma'a aka jibge ƴan sandan ɗauke da makamai a toll gate din na unguwar Lekki bayan sake buɗe hanyar.
Da ma dai gwamnatin Najeriya ta gargaɗi masu yunƙurin sake fitowa tituna da sunan zanga-zangar #Endsars a faɗin ƙasar baki ɗaya, tana mai cewa ba za ta bari a yi zanga-zangar ba.
Mene ne ya faru?
Masu zanga-zanga sun fito suna gudanar da ita a Lekki toll gate da safiyar Asabar.
Sai dai 'yan sandan da aka girke a wurin sun yi musu dirar mikiya inda suka rika dukansu yayin da suka kama wasu daga cikinsu.
Kazalika sun lalata motoci dauke da na'urorin amsa-kuwwa na masu zanga-zangar.
Wasu daga cikin mutanen da aka kama sun shaida wa BBC daga cikin motar da aka jefa su cewa sun je wucewa domin tafiya wuraren aiki ne kawai aka kama su.
Tun 20 ga watan Oktoba aka rufe Lekki toll gate bayan masu zanga-zanga sun yi zargin cewa sojojin kasar sun kashe wasu daga cikinsu.
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce mutum 12 aka kashe a watan na Oktoba a Lekki toll gate da wasu sassan kasar da aka gudanar da zanga-zangar.
'Masu shirin wargaza Najeriya'
A ranar Alhamis Ministan Yaɗa Labarai da Al'adu Najeriya Lai Mohammed, ya yi ga matasan da ke shirin yin zanga-zangar yana mai cewa hakan "ba za ta saɓu ba".
Duk da cewa Lai Mohammed ya ce zanga-zanga na cikin haƙƙin 'yan ƙasa, sai dai ya ce gwamnati ba za ta sake bari a gudanar da zanga-zanga ba da sunan EndSars.
"Gwamnati ba za ta sake bari tashin hankalin da ya faru da sunan zanga-zangar EndSars ya sake faruwa ba a faɗin ƙasar nan a watan Oktoban da ya wuce," in ji ministan.
"Ba za a sake bari wani ya lalata garuruwa ba ko kuma ya ƙuntata wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
"Zanga-zangar EndSars ta watan Oktoba ma ta fara ne cikin kwanciyar hankali. Gwamnati ba ta tsangwame su ba a duk tsawon lokacin da suke yin ta lumana...amma sai wasu suka yi amfani da ita domin tayar da fitina."
Ministan ya ƙara da cewa gwamnati ta bankaɗo wani shirin haɗin gwiwa tsakanin wasu masu fafutika a Najeriya da 'yan ƙasashen waje "domin wargaza Najeriya".