Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
#OcuupyLekkiTollgate: Gwamnati ta gano masu shirin wargaza Najeriya da sunan zanga-zanga - Lai Mohammed
Gwamnatin Najeriya ta gargaɗi masu yunƙurin sake fitowa tituna da sunan zanga-zangar #Endsars a faɗin ƙasar baki ɗaya, wadda wasu matasa suka ƙudiri aniyar yi ranar Asabar mai zuwa.
Ministan Yaɗa Labarai da Al'adu Lai Mohammed, shi ne ya yi gargaɗin yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis, yana mai kakkausan gargaɗi ga matasan cewa "ba za ta saɓu ba".
A farkon makon nan ne dai aka fara kiraye-kirayen sake ɓarkewar zanga-zangar a shafukan zumunta, wadda aka yi wa laƙabin #OcuupyLekkiTollgate a Jihar Legas da ke kudancin ƙasar.
Masu zanga-zangar sun sha alwashin yi wa mashigar Lekki Toll Gate tsinke, wajen da ake zargin sojojin Najeriya sun yi harbe-harbe a kan masu zanga-zangar EndSars a watan Oktoban 2020.
Matasan sun ce suna ƙoƙarin yin hakan ne a matsayin martani ga yunƙurin da gwamnati ke yi na sake buɗe mashigar tare da bai wa kamfanin Lekki Concession izinin ci gaba da harkokinsa, suna masu cewa sai an yi wa waɗanda aka zalunta adalci.
Duk da cewa Lai Mohammed ya ce zanga-zanga na cikin haƙƙin 'yan ƙasa, sai dai ya ce gwamnati ba za ta sake bari a gudanar da zanga-zanga ba da sunan EndSars.
"Gwamnati ba za ta sake bari tashin hankalin da ya faru da sunan zanga-zangar EndSars ya sake faruwa ba a faɗin ƙasar nan a watan Oktoban da ya wuce," in ji ministan.
"Ba za a sake bari wani ya lalata garuruwa ba ko kuma ya ƙuntata wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
"Zanga-zangar EndSars ta watan Oktoba ma ta fara ne cikin kwanciyar hankali. Gwamnati ba ta tsangwame su ba a duk tsawon lokacin da suke yin ta lumana...amma sai wasu suka yi amfani da ita domin tayar da fitina."
Ministan ya ƙara da cewa gwamnati ta bankaɗo wani shirin haɗin gwiwa tsakanin wasu masu fafutika a Najeriya da 'yan ƙasashen waje "domin ɗaiɗaita Najeriya".
Hukumomi a Najeriya sun ce an kashe 'yan sanda 37 da sojoji guda shida da kuma fararen hula 57 sakamakon zanga-zangar ta EndSars a watan Oktoba da ya gabata.
Matasa sun hau kan tituna ne da zummar yin Allah-wadai da cin zarafin da 'yan sanda ke aikatawa musamman na rundunar SARS mai yaƙi da fashi da makami, wadda gwamnati ta rushe bayan zanga-zangar.
Yadda zanga-zangar EndSars ta zama rikici
Zanga-zangar ta EndSARS, wadda aka fara a Legas da Abuja, ta kuma fantsama zuwa wasu jihohin kasar, kafin daga bisani ta rikiɗe ta koma rikici, abin da ya janyo asarar rayuka da dukiyoyin jama'a.
Wasu ɓata-gari da ake zargin sun fake da zanga-zangar sun rika rusa gine-ginen gwamnati da na wasu 'yan siyasa musamman a jihar Legas da ke kudu maso yammacin kasar.
Hukumomi sun baza jami'an ƴan sandan kwantar da tarzoma domin shawo kan lamarin, sai dai tashin hankali ya ci gaba da ƙaruwa sakamakon kisan masu zanga-zanga a Lekki.
Masu zanga-zangar sun zargi jami'an tsaro da buɗe masu wuta a Lekki da ke jihar Legas, wato cibiyar gudanar da zanga-zangar, abin da ya janyo jikkatar mutane da dama.
Wasu dai na ganin buɗewa masu zanga-zangar wuta ya taimaka wajen kazantuwar lamarin musamman a jihar ta Legas.