Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
EndSars: Yadda zanga-zangar EndSars za ta shafi tattalin arzikin ƙasashen Afirka
Wata babbar illa da zanga-zangar nuna adawa da zaluncin 'yan sanda da ta rikiɗe ta zama tarzoma a Najeriya, ita ce yadda take shafar wasu ƙasashen Afirka.
Najeriya dai ita ce kan gaba ta fuskar girman tattalin arziki a nahiyar don haka akwai gagarumar fargaba kan tasirin da zanga-zangar za ta yi ga tattalin arzikin ƙasashe da dama.
Yanayin da tattalin arzikin Najeriyar ya shiga sakamakon zanga-zangar, ya shafi wasu daga cikin kasashen Afirka, daya daga cikin wadannan kasashe ita ce kasar Ghana.
A cewar Majalisar Dinkin Duniya, Ghana na shiga da kaya Najeriya wanda aka kiyasta cewa zai kai dala miliyan dari a duk shekara.
Yawan al'ummar da Najeriya ke dashi da kuma arzikin danyen man fetur, na daga cikin dalilin da yasa take d amuhimmanci wajen tafiyar da harkoki a yammacin Afirka.
Najeriya dai na bawa kasashen kamar Ghana iskar gas don samar da wutar lantarki, sannan mafi yawancin 'yan kasuwar kasar na samun kayayyaki daga Ghanan.
Wani masani kan harkokin kasashen duniya ya ce wannan zanga-zangar zata shafi bangarori da dama musamman ta fuskar tattalin arziki zai shafi cinikayya,
Haka harkokin ua da kulluma ma zasu tsaya saboda otel da bankuna za su tsaya cak, haka shima bangaren kasuwar hannayen jari zai tabo kadan inji masanin harkokin kasashen duniyar.
Ya ce hatta bangaren tsaro ma zai tabo, domin idan har aka samu rikici a Najeriyar, to ko shakka ba bu mutane da dama zasu tsere daga kasar.
Najeriya dai ita ce kashin bayan Afirka a saboda haka zaman lafiya ke da muhimmanci bama ga kasar kadai ba, har ma na nahiyar.