Juyin mulkin Myanmar: Dubban masu zanga-zanga sun yi arangama da ƴan sanda

Asalin hoton, Reuters
Ƴan sanda a babban birnin Myanmar Nay Pyi suna amfani da ruwan zafi wajen fesa wa dubban ma'aikata da ke zanga-zangar adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar.
Zanga-zangar da dubban mutane ke yi a tituna a faɗin ƙasar ta shiga kwana na uku, inda suke kira da a saki zaɓaɓɓiyar shugabar ƙasar Aung San Suu Kyi kuma a koma turbar dimokraɗiyya.
Kafar talbijin ta ƙasar ta yi wa masu zanga-zangar gargaɗi cewa za a ɗauki mataki a kansu idan suka yi wa zaman lafiyar al'umma barazana ko kuma idan "suka karya doka."
Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan da aka fara gagarumar zanga-zangar da aka shafe kusan shekara 10 ba a yi ba a Myanmar.
A makon da ya gabata ne sojoji suka ƙwace mulki, inda suka ce sun yi hakan ne bisa zargin yin maguɗi a zaɓen da aka gudanar tun da fari, amma ba su gabatar da hujjar zargin ba.
Sun kuma sanya dokar ta ɓaci har ta tsawon shekara guda a Myanmar, sannan aka miƙa mulkin ƙasar ga babban kwamandan rundunar askarawan ƙasar Min Aung Hlaing.
An yi wa Ms Suu Kyi ɗaurin talala tare da wasu manyan jami'an jam'iyyarta ta National League for Democracy Party (NLD), da suka haɗa da shugaban ƙasa Win Myint.
- Aung San Suu Kyi: Yadda ƙimar shugabar da ta goyi bayan yi wa Musulmai kisan kiyashi a Myanmar ta zube
- Aung San Suu Kyi: Sojojin Myanmar sun hamɓarar da shugabar da ta goyi bayan yi wa Musulman Rohingya kisan kiyashi
- Aung San Suu Kyi : Sojojin da suka hamɓarar da shugabar da ta goyi bayan kisan Musulmai sun naɗa ministoci
'Ba za mu je aiki ba'
Dubun-dubatar mutane ne suka taru a ranar Litinin da safe a birnin Nay Pyi don nuna cewa suna yajin aiki, inda wasu biranen ma kamar su Mandalay da Yangon uka bi sawu, a cewar sashen BBC Burma.
Masu zanga-zangar sun haɗa da malaman makaranta da lauyoyi da ma'aikatan banki da ma'ikatan gwamnati.
Wani bidiyo ya nuna yadda yan sanda ke watsa wa masu zanga-zangar ruwan zafi a Nay Pyi, inda suke ta murtsuka idanuwansu, suka kuma jiƙe sharkaf.
Kyaw Zeyar Oo, wanda ya ɗauki bidiyon ya shaida wa BBC cewa, motocin ƴan sanda biyu da ke watsa wa masu zanga-zangar ruwan ba su yi wani gargaɗi ba kafin su fara, a yayin da mutanen ke zanga-zangar tasu cikin lumana a gaban ƴan sandan.
Ya ƙara da cewa zuwa ranar Litinin da rana lamarin ya lafa, bayan da masu zanga-zanga suka ci gaba da taruwa, amma har a lokacin motocin fesa ruwan suna nan.
Rahotanni na cewa wasu mutane kaɗan sun ji raunuka, sannan babu rahotannni tashin hankali a wasu wuraren.

Asalin hoton, Reuters
A intanet kuwa ana ta kiraye-kirae ga ma'aikata da su bar wuraren aiki su tafi wajen zanga-zanga.
"Yau ranar aiki ce amma ba za mu je ba ko da kuwa za a yanke mana albashi," in ji wani mai zanga-zanga, Hnin Thazin mai shekara 28 da yake aiki a wata masana'antar yin kayan sawa, kamar yadda ya shaida wa AFP.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Wakilin BBC a Kudu maso Gabashin nahiyar Asiya Jonathan Head ya ce gagarumar zanga-zangar da aka gudanar a ƙarshen makon da ya gabata ta ƙara wa mutane da dama da ke adawa da juyin mulkin azama, duk da cewa har yanzu ba a san jagororin zanga-zangar ba, a yanzu dai ana yi mata kallon wani abu da dukkan masu yi ke da hannu a ciki a wani mataki na nuna fushi.
Sai dai har yanzu babu martani daga sojojin da suke mulkin ƙasar, sannan ƴan sanda ma kamar ba su da alƙiblar yadda za su yi da masu zanga-zangar don sun fi su yawa, a cewar wakilinmu.

Asalin hoton, Getty Images
A makon da ya gabata, sojojin Myanmar sun ƙwace ikon ƙasar bayan zaɓen da aka yi wanda jam'iyyar NLD ta yi nasara.
Sojojin suna goyon bayan jam'iyyar adawa ne, wacce take son a je zagaye na biyu na zaɓen, tana mai zargin an tafka maguɗi.
Hukumar zaɓe ta ce babu wata hujja da za ta tabbatar da iƙirarin.
An yi juyin mulkin ne yayin da ake daf da fara sabon zama a majalisar dokoki.


Sojojin sun sauya ministoci da mataimakansu da suka haɗa da na kuɗi da na lafiya da na harkokin cikin gida da ƙasashen waje.
Sun kuma toshe kafar Facebook, wacce ake yawan amfani da ita a faɗin ƙsar, da Tuwita da Instagram.
Amma hakan bai yi nasarar hana zanga-zangar da ake yi a ƙasar tun ranar Asabar da Lahadi ba - wacce ita ce mafi girma da ƙasar ta gani tun shekarar 2007, lokacin da dubbai suka nuna adawa da mulkin soji.











