Kauyen Uromi: Yadda kungiyoyin matan kauyen suka yi zanga-zanga don a kori Fulani daga Edo

Ana zargin makiyayan da garkuwa da mutane

Asalin hoton, OTHER

Bayanan hoto, Ana zargin makiyayan da garkuwa da mutane

Kungiyoyin mata daban-daban ne suka fantsama kan titunan wani kauye a jihar Edo da ke kudancin Najeriya suna zanga-zanga domin hukumomi su kori Fulani makiyaya daga jihar.

Lamarin ya faru ne a yau Laraba.

Matan sun yi zargin cewa makiyaya suna yin garkuwa da jama'ar yankin domin karbar kudin fansa.

Sun yi cincirindo inda suka toshe hanyoyi suna kira ga mahukunta su dauki mataki a kan makiyayan.

Kodayake ba mu samu magana da makiyayan yankin ba, amma rahotanni sun ce sun musanta wannan zargi.

Wani mazaunin jihar ta Edo ya shaida wa BBC Hausa cewa lamarin ya sa hankula sun tashi domin ana fargabar barkewar tarzoma.

Shugaban 'yan arewa mazauna jihar, Alhaji Badamasi Saleh, ya gaya mana cewa mazauna jihar sun dade suna zargin makiyaya da yin garkuwa da jama'a domin karbar kudin fansa.

A cewarsa, kwanakin baya ma sai da aka kama wasu Fulani ana zarginsu da sace wasu 'yan asalin jihar.

Wani jami'in gwamnatin jihar Surahaisu Usman ya shaida mana cewa yanzu hankula sun kwanta yana mai cewa ba za su bari wani ko wata su karya doka ba.

Mata masu zanga-zanga

Asalin hoton, OTHER

Wannan lamari na faruwa ne kwanaki kadan bayan an yi sulhu tsakanin makiyaya da mazauna jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya bayan gwamnan jihar ya ba su wa'adin ficewa daga dazukan jihar.

Ya yi zargin cewa suna amfani da dazukan ne a matsayin mafakar ajiye mutanen da suke yin garkuwa da su.

Sai dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnan ba shi da hujjar korar kowanne dan kasar daga inda yake zaune.

Kazalika a jihar Oyo da ke makwabtaka, wani mai rajin kare hakkin Yarbawa, Sunday Igboho, ya umarci makiyaya su bar kasashen Yarbawa saboda zargin da yake yi musu da yin garkuwa da jama'a.

Sai dai makiyayan sun sha musanta zarge-zargen suna masu cewa ana so a yi musu kora da hali ne kawai.

Hasalima wasu makiyaya sun yi zargin cewa ana kashe su domin kawai zargin da ake yi wa wasu bara-gurbi daga cikinsu.