Rikicin Yemen : Majalisar Dinkin Duniya ta buƙaci tsagaita wuta

Asalin hoton, AFP
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira ga sojojin gwamnatin Yemen da 'yan tawayen Houthi da su daina ɓarin wuta a Hodeida da ke yammacin kasar.
Da dama daga cikin mayaka daga bangarorin biyu sun mutu a ƙazamin faɗan da aka kwashe tsawon kwanaki ana yi.
Jami'an Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta shekaru biyu sun ce tilas ne a dakatar da yakin tun kafin abin ya kai ga shafar fararen hula.
Babu wani cikakken bayani da aka bayar game da irin asarar rayukan fararen hula da aka yi.
Tashar jiragen ruwa ta Hodeida wacce ke hannun 'yan tawaye muhimmiyar hanya ce ta shigar da abinci da kayan agaji a kasar da dubun dubatan mutane ke cikin yunwa bayan shekaru ana yaki.
Yemen ta fara fuskantar yaƙin basasan da ya ta'azzara ne a watan Maris din 2015, lokacin da 'yan tawayen Houthi suka kwace iko da mafi yawan yammacin kasar suka kuma tursasa wa Shugaba Abdrabbuh Mansour tserewa daga kasar.
Bayan Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da wasu kasashen Larabawa bakwai suka farga da bunkasar wata kungiya da suka yi amannar Iran na goyawa baya, sai suka fara wata fafutuka da nufin dawo da gwamnatin Mista Hadi.
A watan Satumba ne kwararrun MDD kan Yemen suka ce akwai kwararan hujjojin da ke tabbatar da sojojin rundunar da Saudiyyar da masu goyon bayan gwamnatin Yemen sun aikata laifukan yaki da suka hada da:
- Kai hare-haren soji a kaikaice, sabanin abin da dokar rarrabe tsakanin mutane ta yi tanadi.
- Kai hare-haren sama sabanin dokar rarrabewa tsakanin mutane da lura da girman illar da hakan.
- Kisan kai, azabtarwa, cin zarafi, musgunawa, fyade da cin mutunci ta hanyar kin gurfanarwa a gaban kotu da kuma daukar yara 'yan kasa da shekara 15 aikin soji ko kuma amfani da su a matsayin mayaka.
Rahoton ya kuma zargi 'yan tawayen Houthi da aikata laifukan yaki da suka hada da kai wa fararen hula hari da harbin mai uwa da wabi da aikata kisan kai da azabtarwa da yin garkuwa da mutane da kuma amfani da kananan yara a matsayin mayaka.











