Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal vs Newcastle: Abin da ya kamata ku sani kan fafatawar da kungiyoyin za su yi
Arsenal za ta karbi bakuncin Newcastle United a wasan mako na 19 a gasar Premier League ranar Litinin a Emirates.
Arsenal tana mataki na 11 a kan teburi da maki 24, ita kuwa Newcastle tana mataki na 15 sannan tana da maki 19.
Abubuwan tarihi da suka fara tsakanin Arsenal da Newcastle
Arsenal ta lashe wasa 14 daga 15 da ta fafata da Newcastle a Premier League, amma a watan Afirilu ne Newcastle ta ci Arsenal 1-0.
Newcastle United ta yi rashin nasara a wasa takwas a jere a gidan Gunners, tun bayan cin 1-0 da ta yi a watan Nuwambar 2010.
Ranar 9 ga watan Janairu Arsenal ta fitar da Newcastle United daga gasar FA Cup da ci 2-0.
Kokarin Arsenal a bana
Gunners ta samu maki 10 daga 12 da suka kamata ta hada tun Kirsimeti, inda ta ci karawa uku da canjaras daya.
Watakila ta yi wasa na biyar ba tare da kwallo ya shiga ragar Arsenal ba a karon farko, tun bayan bajintar wasa shida daga Janairu zuwa Fabrairun 2009.
Gunners ta yi nasara a karawa shida a Premier League da ta buga a gida ranar Litinin har da wadda ta doke Newcastle cikin watan Afirilun 2019.
An doke Arsenal sau hudu a bana a Premier League a Emirates, kamar yadda aka yi mata a 2010/11. Sai dai ba a doke ta ba fiye da hakan tun bayan 1994/95 lokacin da take Highbury.
Gunners ba ta zura kwallo ba a raga a wasa bakwai a kakar bana, kawo yanzu ta yi shekara biyar rabon da ta kasa cin kwallo a fafatawa takwas a Premier League.
Pierre-Emerick Aubameyang ya ci Newcastle a kowanne wasa uku da ya fuskanci kungiyar.
Kwazon Newcastle United
Newcastle United ba ta ci wasa takwas ba a dukkan karawa, tun bayan da ta doke West Brom a Premier League ranar 12 ga watan Disamba, inda ta yi canjaras biyu da rashin nasara shida.
Newcastle ta ci kwallo daya tal a wasa shida baya da ta fafata.
Za kuma ta yi rashin nasara a karo na uku a farko shekara idan Arsenal ta doke ta, rabonda ta yi hakan tun 1989.
Newcastle United ta yi rashin nasara a wasan waje biyar a jere a karon farko, tun bayan da aka doke ta sau 10 daga Disambar 2015 zuwa Afirilun 2016.
Newcastle ta ci wasa biyar daga tara da ta buga da kungiyoyin cikin Landan.
Koci Steve Bruce bai yi nasara a karawa 17 da ya buga a waje da Arsenal a matakinsa na koci a dukkan kungiyoyin da ya horar, inda ya yi canjaras hudu aka doke shi wasa 13.