Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Harry Kane na kan gaba a cin Arsenal a karawa da Tottenham
Tottenham ta yi nasara a kan Arsenal da ci 2-0 a wasan mako na 11 a gasar Premier League da suka fafata ranar Lahadi.
Heung-min Son ne ya fara cin kwallo a minti na 13 da fara tamaula, sai Harry Kane ya kara na biyu daf da za su je hutu.
Kawo yanzu Kane ya ci Arsenal kwallo 11 kenan a dukkan fafatawa da suka yi, kuma shi ne kan gaba a Tottenham wajen cin Gunners a tarihi.
Kafin nan Emmanuel Adebayor da kuma Bobby Smith ne kan gaba a Tottenham wajen zura kwallo a ragar Arsenal.
Wasa na bakwai kenan da kungiyoyin suka kara a gasar Premier League a gidan Tottenham wadda ta ci wasa biyar da canjaras biyu kawo yanzu.
Kuma fafatawa ta 11 da Mourinho ya yi a gida da Arsenal ba ta yi nasara a kan kocin ba.
Mikel Arteta ya yi kan-kan-kan da Bertie Mee wanda ya yi rashin nasara a jere a wasan na hamayya a kakar 1966/67.
A wasan da Arteta ya ja ragamar Gunners a fafatawa da Tottenham a bara rashin nasara ya yi.
A fafatawar da Arsenal ta yi rashin nasara karo biyu a jere a hannun Tottenham ita ce sau biyu a Mayun 1993 da kuma a Nuwambar 2010.
Da wannan sakamakon Tottenham ta koma mataki na daya a kan teburin Premier League da maki 24, bayan buga wasa 11.
Arsenal ma karawa 11 ta yi a gasar bana, ta hada maki 13 tana mataki na 15 a kasan teburi.
Ranar Alhamis 10 ga watan Disamba, Arsenal za ta ziyarci Dundalk a wasa na shida-shida a cikin rukuni a gasar Europa League.
A kuma ranar Tottenham za ta karbi bakuncin Royal Antwerp a dai wasan karshe na cikin rukuni a gasar ta Zakarun Turai.
Wadanda suka yi alkalancin wasan Premier ranar Lahadi::
Alkali: Martin Atkinson Mataimakansa: Adam Nunn da kuma Constantine Hatzidakis. Mai jiran ko ta kwana: Andre Marriner. Mai kula da VAR: Kevin Friend. Mataimakinsa: Mark Scholes.