Zaɓen Uganda : Ana zargin an tafka maguɗi a zaɓe

Mahukuntan a Uganda sun yaba da zaɓen da aka gudanar a ranar Alhamis, tare da bayyana shi a matsayin na gaskiya da gaskiya, duk da zargin maguɗi da babban ɗan takarar adawa, Bobi Wine ya yi.

Wani mai magana da yawun shugaba mai ci Yoweri Kaguta Museveni wanda ke neman tsawaita wa'adin mulkinsa na shekara 35, wato Don Wanyama, ya ce ba a gabatar da shaidar yin magudi ba.

Ya ce sojoji da aka tura gidan Bobi Wine sun je ne don tabbatar da tsaron lafiyarsa a matsayinsa na babban ɗan takara.

Shugaban ƴan adawar ya bayyana zaɓen shugaban kasar a matsayin shirme kuma ya la'anci kasancewar sojoji a a gidansa, yana bayyana hakan a matsayin barazana.

Ya ce zai gabatar da ƙwararan hujjujin da za su nunawa duniya irin cuwa-cuwar da aka yi a zaɓen da zarar an dawo da Internet da aka katse a dukkanin faɗin ƙsar.

Yayin da aka ƙidaya fiye da rabin ƙuri'un da aka kada, shugaba Museveni na kan gaba da rata mai yawan gaske.

Shugaba Museveni mai shekara 76 yana fuskantar 'yan takara 10, amma fafatawar ta fi zafi tsakaninsa da Robert Kyagulanyi, wanda aka fi sani da Bobi Wine, mai shekara 38 a duniya.

Ranar Talata, hukumar da ke sanya ido kan kamfanonin sadarwar Uganda ta umarci kamfanonin su rufe shafukan sada zumunta, sa'o'i kadan bayan Facebook ya rufe shafukan "bogi" wanda ya ce suna da alaka da gwamnatin kasar.

Facebook ya ce ana yin amfani da shafukan wajen sauya ra'ayin 'yan kasar game da zaben da za a gudanar.

Masu amfani da shafukan sada zumunta sun soma bayyana samun tsaiko a shafukan Twitter, WhatsApp, Instagram da Snapchat ranar Talata.

Twitter ya mayar da martani da cewa hakan keta hakkin masu amfani da intanet ne.

Kamfanonin dillancin labaran AFP da Reuters sun ambato jami'an hukumar da ke sanya ido kan kamfanonin sadarwa na Uganda suna cewa an dauki matakin ne domin yin raddi ga Facebook a kan rufe shafukan da ke da alaka da gwamnatin kasar.