Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yoweri Museveni: Ma’anar sabon sunan shugaban ƙasar Uganda
Shugaban ƙasar Uganda, wanda aka sani da suna Yoweri Kaguta Museveni, yanzu ya ƙara sunansa na ƙuruciya, Tibuhaburwa, a cikin jerin sunayensa.
Sunan yana nufin "mutumin da ba ya daukar shawara ko gyara" a yarensa na Runyankore.
Sauya sunan ya janyo yin shaci-faɗi da raha a shafukan intanet na Uganda, inda wasu ke tambaya kan aikin masu ba shi shawara.
Shugaban ƙasar ya sanya hannu a kan wasu takardun rantsuwa waɗanda ke nuna cewa daga yanzu za a riƙa kiransa da suna Yoweri Tibuhaburwa Kaguta Museveni.
Duk da yake an sha kiransa da wannan suna a cikin shekara 34 da ya kwashe yana mulkin ƙasar Uganda, bai taɓa yin amfani da sunan ba a bainar jama'a.
Wasu bayanai da aka fitar ranar 6 ga watan Oktoba sun ambato Shugaba Museveni yana cewa sunan yana cikin sunayen da yake amfani da su a takardunsa na makaranta.
Sai dai an yi amannar cewa ya ɗauki matakin ƙara sunan ne saboda buƙatar da Hukumar Zaɓen ƙasar ta yi cewa dole sunayen da 'yan takarar zaɓen 2021 su yi daidai da sunayen da ke jikin takardun makarantunsu.
Kwankin baya Hukumar Zaɓen ta bayar da sanarwa cewa ba za ta amince da mutanen da suka miƙa mata sunayen da suka sha bamban da sunayen da ke cikin takardun makarantunsu.
A shekarar 2017, wata ta soke zaɓen wani ɗan majisar dokokin ƙasar saboda sunayen da ya miƙa yayin tsayawa takara sun sha bamban da sunayensa da ke jikin takardunsa na makaranta.
A watan Yuli ne Shugaba Museveni mai shekara 75, wanda ya kwashe shekara 36 yana mulkin Uganda, ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a zaɓen shekarar 2021.